Diébédo Francis Kéré: Dan Afirka na farko da ya samu lambar yabon ilimin zane-zane

Diébédo Francis Kéré

Asalin hoton, Lars Borges

Diébédo Francis Kéré, dan Burkina Faso ne da ya yi shuhura a fagen zane-zanen gidaje, ya zama dan Afrika na farko da ya lashe kyautar nan ta Pritzker mai daraja, wadda ake wa kallon daidai da ta Nobel a fagen zane-zanen gidaje.

Aikinsa da yake yi tuƙuru, ciki har da gidajen da ya zana a kasarsa ta haihuwa da kuma wasu a fadin Afrika da Turai da Amurka na daga cikin abubuwan da suka ba shi wannan dama.

Mr Kéré, mai shekara 56, ya yi matukar farin ciki da karbar wannan kyauta wadda ake dauka a matsayin mafi daraja a aikinsu, ya kuma ce a yanzu "shi ne mutumin da ya fi kowa farin ciki a fadin duniya".

Nasarar tasa ta gomman shekaru na ta fuskanci kalubale tun daga takaitattun damarmakin da ya rika fuskanta a kauyen da ya fito.

"Na tashi a kauyen da babu makarantun yara, 'yan kauyenku su ne 'yan uwanku," kamar yadda ya shaida wa kyautar Pritzker.

"Ina iya tuna wani dan karamin daki da kakata ke zama ciki tana mana tatsuniya da a-ci-bal-bal ciki, yayin da muke wasn jefe-jefe ita kuma muryarta na kai wa har inda muke na kiranmu mu matso kusa da ita musa wurin zama. Anan na fara samun tunanin zama mai zane-zanen gidaje.

Lokacin yana shekara bakwai, Mr Kéré ya tsinci kansa a wani ajin makaranta mai matukar zafi da yake dauke da yara sama da 1000.

A matsayinsa na yaron farko a kauyensu da ya fara zuwa makaranta, wannan matsattsen wajen karatun da ya zauna na daga cikin abubuwan da suka kara masa azama ta fuskar ilimi don inganta rayuwar yaran Burkina Faso.

Shekaru masu yawa bayan ya dawo daga Jamus, mafarkinsa ya zama gaskiya, Mr Kéré ya zana wata makaranta firaimare a kauyensu na Gando a matsayin gininsa na farko a 2001.

An gina ta ne da taimakon mutanen yankin, wadda suka taimaka da karfinsu da kuma kayan aiki kamaraka wallafa a shafinsu.

Gandp Primary School. There are 6 children in the photo. There are colourful shutters behind them.

Asalin hoton, Erik-Jan Owerkerk

Gando Primary school. The building has many windows and yellow shutters. it has a flat roof.

Asalin hoton, Erik-Jan Owerkerk

Gando Primary School. There are colourful shutters and trees in the background. There are two girls walking past it.

Asalin hoton, Erik-Jan Owerkerk

Shirin nasarar da makarantar ta samu a 2004, wanda aka bayar da shekaru uku domin samar da ginin da al'umma yankin da musulmai suka fi yawa ciki suke so.

Ba da aikin wannan makarantar ya share masa fa na kara zana wasu gine-ginen makarantu kamar su Lycée Schorge, itama da ke Burkina Faso.

Students in Lycée Schorge secondary school. Beams of light are entering the building.

Asalin hoton, Francis Kéré

Daya daga cikin abin da ya sanya ayyukan Mr Kéré suka zama na daban shi ne yadda yake amfani da fitila, wanda masu kyautar suka sanar.

"Mawakin ya nuna wuta daya ce daga cikin abubuwan da suke ba sa sauyawa shi ne haske.

"'Ya'yan rana kan ratsa gine-ginensa, akan samun baranda da kuma wuraren hutawa, wanda yake maganin zafi ko kuma yawan cinkosn da mutane ke yi a wuri guda."

Lycée Schorge Secondary School at night. There are light on in the building and trees in the forefront of the picture.

Asalin hoton, Iwan Baan

Women walking outside Lycée Schorge Secondary School. There are bikes in the background. The building is made up of tall brown sticks.

Asalin hoton, Iwan Baan

Mr Kéré' yadda yake amfani da wannan haske ya tabbata a gine-ginen da ya yi a cibiyoyin lafiya, Kamar su ginin Social Welfare da Kauyen Opera da har yanzu ke ci gaba da ginawa.

Centre for Health and Social Welfare. There are beds lines up with white nets covering them. The walls are brick and there is light entering from small windows.

Asalin hoton, Francis Kéré

Bayan gine-ginensa a Burkina Faso, wanda ya lashe kyautar ya kuma zana wasu gune-gine na dindindin da kuma na wucin gadi a Turai da Amurka, kamar ginin Serpentine Pavilion na Landan da ya yi a 2017.

Ko wacce shekara, Serpentine Gallery na gayyato mutane da kasashen waje domin su zo Lamdam su yi gininsu na farko a birnin.

Tunanin zanesa ya samo asali ne daga wata bishiya a kauyensu na Gando da wani tsarin gini da zai janyo hankalin masu ziyara da kuma shukoki na gaske zagaye da wajen.

Serpentine 2017 structure. It is of a round shape with blue panels around it. It is an open structure.

Asalin hoton, Iwan Baan

Serpentine 2017 pavillion with a view of the open roof.

Asalin hoton, Frances Kéré

Mr Kéré ysa kuma zana fitaccen ginin nan na Coachella Valley Music and Arts Festival, wanda ake amfani da shi ko wacce shekara a California kuma yake jan hankalin mashahuran mutane da wadanda suka yi suna a masana'antar nishadantarwa kamar su Billie Eilish, da Swedish House Mafia da Kanye West da dai sauransu wadanda za su yi wasa a wannan shekara.

Mr Kéré ya zana filin wasa na shekara shekara a 2019 da ake kira Sarbalé Ke, wanda ke nufin House of Celebration. Kuma wata bishiyar kwalba ce ta fara saka shi tunanin ginin.

Sarbalé Ke structures with hollow interior and colourful patterns on them. There are people sitting inside the hollow interior.

Asalin hoton, Iwan Baan

Likafar gine-ginen Mr Kéré ta ci gaba kuma ya yi gini masu yawa ciki har da zana ginin majalisar Burkina Faso da ta Benin.

Duk da cewa bai kammala ba amma ya zuwa yanzu ginin ya kara fito da yadda yake amfani da haske a gine-ginensa.

A rendered picture of Burkina Faso National Assembly. There is plenty of light entering from the ceiling.

Asalin hoton, Kéré Architecture

Rendered image of Benin National Assembly.

Asalin hoton, Kéré Architecture

Dukan hotunan na da hakkin mallaka.