Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tashin farashin mai da rikicin Ukraine sun shafi farashin dizel a Najeriya
A Najeriya, ana cigaba da fuskantar karancin man fetur a fadin kasar wata matsala da ta kunno kai a baya-bayan ita ce ta karancin man dizel, inda a yanzu haka farashin sa ya tashi zuwa naira 700 a kan kowace lita.
Sai dai wasu masu ruwa da tsaki akan man fetur sun ce matsalar tana da nasaba da tashin da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya.
A baya bayan nan alkalumma sun nuna farashin man dizel ya tashi da kashi 170 cikin shekara guda, a shekarar da ta gabata ana saida lita daya ta man dizel kan farashin naira 240.
Masu ruwa da tsaki akan harkar man fetur, sun danganta tashin da man dizel ya yi da tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya, sakamakon yakin da Rasha ke yi a Ukriane, da kuma cire tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi.
Alhaji Bashir Dan Malam shi ne shugaban dillalan masu sayar da man fetur a shiyyar arewacin Najeriya, ya ce shaidawa BBC cewa dama tuntuni gwamnati ta cire tallafi akan man Dizel da Kalanzir, sannan farashin danyan mai da ake yin dizel da kalanzir da shi ya tashi a kasuwannin duniya.
''Saboda haka dama can 'yan kasuwa ke shigo da shi, to kuma tashin farashinsa da rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine ya taka muhimmiyar rawa wajen tsada da kuma karancinsa. Farashinsa ya banbanta a dukkan rumbunan da ake sauke danyan mai a jihohin Fatakwal, da Warri da kuma Lagos.
A Warri su na saida shi akan naira 600 kowacce lita, sai kuma Lagos su na saidawa 600-610, har zuwa 620, da ya ke 'yan kasuwa ne kowa ya na saidawa ne gwargwadon yadd ya saro shi,'' in ji Bashir.
Amma a nasa bangaren Malam Sulaiman Adamu Dan-Zaki shugaban kungiyar ma'aikatan sufuri ta Najeriya, ya danganta tsadar man Dizel da rashin sanya ido daga mahukuntan kasar.
Dan-Zaki ya ce babu wani takamaimai farashi tsayayye da za a ce ana saida Dizel akai, masu saida man kowa yanko abin da ya ke so ya ke yi, ya kuma saida kan rashin da ya ga dama.
''Wannan bai dace ba, ko da aka cire tallafin mai wajibi ne gwamnati ta yi masa farashi, ta fadawa 'yan kasuwa kada u saida man ya wuce farashi kaza. Saboda idan ba ayi haka ba kasuwar za ta zama kara zube, kamar yadda muke gani a halin yanzu, kowa na abin da ya ga dama. Ko a mutu, ko ayi rai babu ruwansu.''
Tun bayan shigo da gurbataccen man fetur Najeriya a watan Fabrairu, wanda ya janyowa masu ababen hawa matsalar inji da lalata motoci, kasar ta fada cikin matsin rashin man fetur.
Sai kuma ga matsalar tashin farashin man Dizel da yawancin ,manya da matsakaitan masana'antu da tsirarun gidaje suk dogara da shi wajen harkokin yau da kullum.
Farashin iskar gas da na ɗanyen man fetur na hauhawa sakamakon fargabar da rikicin Rasha da Ukraine ke haifarwa game da jigilar makamashin a faɗin duniya.
Farashin ɗanyen mai samfurin Brent, wanda aka fi amfani da shi, ya yi tashin da bai taɓa yi ba cikin shekara bakwai zuwa dala 99.38 kan kowace ganga ɗaya a ranar Talatar da ta wuce.