Wane ne ke so a cire tallafin man fetur a Najeriya?

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Tsawon shekaru da dama, gwamnatoci a Najeriya na cewa suna so talakawansu su sayi man fetur a farashi mai sauƙi ta hanyar ware kuɗi domin ba da tallafi.

Sai dai wasu alƙaluma da gwamnati ke fitarwa sun nuna cewa ana kashe kusan naira biliyan 250 duk wata a matsayin kuɗin tallafi, wanda gwamnati a yanzu ke cewa ya yi yawa kuma tana so ta yi amfani da su a wasu ayyukan raya ƙasa.

Batun cire tallafin ya mamaye kanun labarai a Najeriya a wannan makon, kuma mutane suna ta tsokaci a shafukan sada zumunta.

Duk da cewa wasu gwamnatoci a baya ba su yi nasarar ba a yunƙurinsu na cire tallafin, gwamnatin Shugaba Buhari ta ci alwashin cire shi biyo bayan kafa sabuwar dokar man fetur ta Petroleum Industry Act (PIA), wadda ta mayar da kamfanin na kasuwanci zalla maimakon na gwamnati ita kaɗai.

Sai dai kuma bayanai masu cin karo da juna sun fara ɓulla daga fadar gwamnatin a baya-bayan nan kan cirewa ko barin tallafin, wanda farashinsa zai kai kusan N300 idan gwamnati ta yi nasarar cire shi.

Yayin da Ministar Kuɗi ke cewa an saka ƙudirin a cikin kasafin kuɗi na 2022, shi kuma Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan na cewa Shugaba Buhari ya faɗa masa cewa bai umarci kowa ba ya cire tallafin.

Nan da wata shida za mu daina biyan tallafi - Ministar Kuɗi Zainab Ahmed

A watan Oktoban 2021, Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana wa 'yan ƙasa cewa gwamnati ta shirya domin mayar da harkar man fetur ta 'yan kasuwa zalla, tana mai cewa kuɗin da za a biya tallafi na wata shida na farkon 2022 kawai suka saka a kasafin kuɗi.

"Cikin kasafinmu na 2022, mun saka kuɗin tallafi na watan shidan farko, sauran rabin kuma muna yunƙurin sauya sashen zuwa na 'yan kasuwa don mu dinga adana kuɗaɗen ƙasar waje da kuma samun ƙarin riba daga fetur da iskar gas," in ji Zainab Ahmed.

Ta ƙara da cewa gwamnati na sa ran nan da watan Yuni za ta daina biyan tallafi kwatakwata.

"Idan muka kalli tsabar kuɗi biliyan 250 duk wata, wanda kuma yake ta ƙaruwa, hakan na nufin kamfanin mai na NNPC zai samu ribar biliyan 120 kenan. To yanzu kuma mun fara shiga yanayin da NNPC ba ya iya samar da ribar ko kwandala.

"Idanka tara biliyan 250 sau 12, kusan tiriliyan uku kenan. Idan ba mu cire wannan kuɗin ba to abin da za mu ci gaba da biya kenan. Wannan kuɗi ne da za mu iya amfani da su a ɓangaren lafiya da ilimi."

Ta ce sabuwar dokar man fetur ta PIA ta tanadi cewa "wajibi ne gwamnati ta zare hannunta daga ƙayyade farashiun mai".

A ranar 31 ga watan Disamba Shugba Buhari ya sanya wa dokar kasafin kuɗin hannu bayan mako biyu da majalisun wakilai da ta dattawa suka amince da shi bayan sun kammala nazari da gyare-gyare.

'Za mu raba wa 'yan ƙasa kuɗin tallafin'

Kazalika, ministar ta ci gaba da cewa za a yi amfani da kuɗin tallafin wajen raba wa 'yan Najeriya mafiya buƙata, ta hanyar ba su dubu biyar-biyar a matsayin alawus na sufuri, sannan za a biya kuɗin ne ta hanyar intanet kamar E-Naira da sauransu.

"Za mu zauna mu duba yawan mutanen amma mun amince cewa za mu bai wa mutum miliyan 20 zuwa 40 ta hanyar tura musu ta intanet, Mun fahimci cewa E-Naira za ta taimaka da sauran hanyoyin biyan kuɗi."

Ta ci gaba da cewa za a tura wa mutane kuɗin ne tsawon wata shida zuwa 12.

Sai dai ba ta bayyana takamaiman adadin kuɗin da za a raba wa 'yan Najeriyar ba, tana mai cewa suna ci gaba da tattaunawa.

Buhari bai sa kowa ya cire tallafin fetur ba - Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan

Da yake magana da manema labarai a yammacin Talata bayan gana wa da Shugaba Buhari a Abuja, Sanata Ahmad Lawan ya ce shugaban ƙasa ya faɗa masa cewa bai nemi wani mutum ya bi hanyoyin cire tallafin ba.

"Da yawanmu mun damu da fafutikar baya-bayan nan da zanga-zanga. Mutanen mazaɓarmu sun damu matuƙa cewa gwamnati za ta cire tallafin man fetur, saboda haka a matsayinmu na 'yan majalisa abu ne mai muhimmanci," a cewar Ahmad Lawan.

Sanatan ya ƙara da cewa: "Na ga cewa ya zama dole na ziyarci shugaban ƙasa a matsayinsa na jagora don tattauna abubuwan da suka damu 'yan ƙasa, kuma ina mai farin cikin shaida muku cewa shugaban ƙasa ya faɗa min bai taɓa faɗa wa kowa ba cewa ya kamata a cire tallafin fetur."

Sai dai ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ministar kuɗi ba ta mayar da martani kan kalaman sanatan ba.

Karin wasu labaran masu alaƙa

A ƙara farashi zuwa N305 - Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa

Yayin da ake tsaka da wannan muhawarar, wani rahoto da jaridar intanet ta TheCable ta ruwaito a safiyar Laraba ya ce Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa National Economic Council (NEC) ta bai wa gwamnatin Buhari shawarar ƙara farashin mai nan da watan Fabarairun 2022.

Rahoton ya ce majalisar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, ta nemi a mayar da lita ɗaya ta mai zuwa N305.

Wani kwamati da Gwamna Nasir El-Rufai ke shugabanta ne ya ba da shawarar, kamar yadda jaridar ta ruwaito, inda suke son a ƙara naira 130 zuwa 140 ga kowace lita maimakon 162 zuwa 165 da ake sayarwa a yanzu.

A watan Mayun 2021, Ƙungiyar Gwamnoni ta Najeriya ma ta ba da shawarar a mayar da farashin N385, amma gwamnati ba ta karɓi shawarar ba.

Ko sun sun soke za su iya ci gaba da biyan tallafin - Masanin tattalin arziki

Masana tattalin arziki na ganin cewa duk da dokar PIA ta tilasta wa gwamnati zare hannunta daga ƙayyade farashin fetur, har yanzu gwamnatin na da hanyoyin da za ta fake da su wajen biyan kuɗin.

Dr. Ahmed Adamu masanin tattalin arzikin man fetur ne a Najeriya, ya faɗa wa BBC cewa talakawa ba za su iya rayuwa babu tallafin ba, saboda haka gwamnati ce kaɗai ke da zaɓin cirewa ko barin sa.

"A yadda ake ciki yanzu, dole ne sai an bai wa talakawa tallafin mai saboda ba za su iya sayensa a farashin da kasuwa ta yi masa ba.

"Matsalar ita ce, idan aka ce za a sayar da shi a farashin kasuwa ba na gwmanati ba, to duk sanda darajar naira ta faɗi mai zai ƙara tsada a Najeriya saboda da dala ake sayo shi daga ƙasashen waje.

"Sannan duk lokacin da farashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwar duniya farashinsa ma sai ya tashi a Najeriya."

Masanin ya ƙara da cewa duk da cewa doka ta hana ba da tallafin, gwamnati za ta iya fakewa da wani shiri a gefe da ake kira Physical Expenditure ko wani daban don ci gaba da ba da tallafin.

"Akwai abin da ake kira doka da kuma ra'ayin gwamnati. Gwamnati za ta iya cire shi daga kasafin kuɗi kuma ta ce ta daina bayarwa a hukumance amma kuma ta bi wata hanya daban.

"Saboda haka dai gwamnati ce kaɗai ke da wuƙa da nama ta bayarwa ko soke tallafin fetur," Dr Ahmed Adamu.

Ko ma dai mene ne, tun da dai Shugaba Buhari ba ya so a cire tallafin da zai jawo ƙara farashin mai, alamu na nuna cewa akwai waɗanda ke son a cire bisa dalilai na tattalin arziki ko kuma akasin haka.