Abin da ya sa matasa ke koyon wankan gawa a Birtaniya

Ghusl class in London
Bayanan hoto, Tahreem, daga hannun hagu, ta shirya ajin koyar da Ghusl ga matasa
    • Marubuci, Daga Shabnam Mahmood
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Asian Network

An bullo da wani tsari na koyar wa da matasa yadda ake wankan gawa wato Ghusl a Birtaniya.

Ghusl yadda ake yi wa mamaci wanka tare da sakawa da lullube shi da farin ƙyalle ko kuma likkafani ne gabanin binne shi, kana daya daga cikin wajiban abubuwa da dana ne da ake yi wa mamaci.

Kafin barkewar annobar korona, tsofaffi masu aikin sa kai ne a cikin al'ummar Musulmi ke gudanar da irin wannan al'ada.

Amma da daman su har yanzu na yi wa kansu garkuwa don kare kansu daga cutar korona.

Yanzu Supporting Humanity, wata kungiyar kulawa da masu alhini na gudanar da taron bita ga matasa masu aiki sa kai don gudanar da wankan gawa a bisa tsarin addinin Musulunci.

Jagorar ayyukan kungiyar Tahreem Noor, ta shaida wa BBC cewa, "yunkurin ya samo asali ne tun bayan barkewar annobar lokacin da adadin wadanda ke mutuwa ya karu" kuma suna "bukatar karin mutane da ke taimakawa da gudanar da jana'iza.

Har ila yau ana gudanar irin wannan a fadin kasar.

Presentational grey line

Mene ne Ghusl?

Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, Ghusl wani yanayin daura alwala ne, ko wanka, da ya ƙunshi tsaftace jiki daga ƙazanta.

Akwai wankan kashi daban-daban, kamar na bayan ɗaukewar jinin haihuwa da jinin al'ada.

Wanda ake yi wa mamaci Musulmi ana kiran sa Ghusl Mayyit wato wankan gawa.

Galibi dangin suke da jinsi daya da mamacin ne ke gudanarwa. Ya kunshi wanke dukkan sassan jiki da sabuly da ruwa ta hanyoyi na musamman na mutunta gawar.

Presentational grey line

"Muna bukatar akalla masu aikin sa kai shida a kan ko wane wankan mamaci," in ji Salma Patel, ta kungiyar Supporting Humanity, wacce ke koyarwa tare da gudanar da wankan Ghusl, kamar yadda ta shaida wa BBC.

Lokacin kullen korona, ta bayyana cewa an haramta wa iyalai da dama yi wa 'yanuwansu jana'iza. An bar wa masu aikin sa kai kamar ta wankewa tare da yi wa mamata ukun jana'izar a rana lokacin tsananin yaduwar annobar.

"Mu kan samu kiran waya zuwa a taimaka lokacin jana'iza, cikin lokaci kankane," ta bayyana.

Lokutan farkon annobar, akwai karancin fadakarwa game da ƙwayar cutar, da kuma ko shin akwai hadarin kamuwa da cutar ta korona daga mamacin.

Kungiyoyin Musulmai da dana, da suka hada da Majalisar Musulmai ta Birtaniya, sun fitar da ka'idojin da za a bi wajen yi wa mamatan da ake tunanin cutar korona ce ta hallaka wanka.

A lokacin, Hukumar Kula da Lafiyar Al'umma ta Ingila ta bayar da shawara kan gudanar da wankan mamaci da sutura a bisa tsarin da addini ya tanada muddin dai za a cigaba da saka kayan kariya a jiki, da kuma bin dokar bayar da tazara.

Ghusl class in London
Bayanan hoto, Kusan mata 90 ne suka halarci taron a Landan

Cutar korona ta yi matukar fi shafar l'ummar kasashen yankin kudancin Asiya.

Dubbai sun mutu daga kwayar cutar, kuma shi ya sa Saffiyah ta yanke shawarar halartar taron bitar kan wankan gawa a Gabashin London.

"Mun rasa rayukan 'yanuwanmu da dama lokacin annobar, kuma zuwa jana'aiza da kuma rashin sani me za ka yi wani abin a tashi tsaye ne,'' ta ce.

Daya mai halartar taron, Khadija, mai shekaru 23, na ganin yana da matukar muhimmanci a koyarwa da matasa irin wannan tsarin saboda, in ji ta.

"Muddin ba mu koya ba, wa zai rika wanke gawawwakinmu ta wannan hanyar?"

Mata 90 ne suka halarci taron bitar mata Musulama a Cibiyar Belgrave Community Centre da ke Gabashin London.

An nuna musu hanyoyin yi wa mamaci wanka da kumma sutura a jikin manyan 'yartsanoni .

Summaya ta bayyana cewa ba ta san cewa ana rufe tsiracin gawa ba da tsumma lokacin wankan, saboda a matsayinta da matashiya Musulma ta damu "game da tsiraci bayan mutuwa".

Mata matasa da suka halarci taron, sun bayyana cewa sun karu sosai da koyarwar, kuma suna jin cewa wannan wani bangare ne na addininsu.

Farzana ta bayyana abubuwan da ta koya da cewa: "A duk lokacin da mutum ya mutu ana kiransa gawa - ka kan rasa sunaka, da matsayinka, da komai naka'".

Kungiyar Supporting Humanity ta ce annobar wata ''matashiya ce'' lokacin da tsofafi suka kasa gudanar da aikin, kana tana kallon haka a matsayin wani sabon tsari ga matasa da za su bayar da gudunmowa a kai a cikin al'ummarsu.

Presentational grey line