Yadda wata mahaifiya ta gano danta bayan shekara 47 da rabuwarsu

Asalin hoton, EBS
Wani dan kasar Eritrea da aka raba shi da mahaifiyarsa shekara 47 da ta gabata ya sake ganin mahaifiyar tasa a Habasha.
Mahaifiyarsa Zenebech ta bayyana a tashar talabijin ta EBS ta kasar Habasha a 'yan kwanakin da suka gabata inda ta ce addu'arta a kullum ita ce "ina son ganin dana kafin na mutu."
Jim kadan bayan wannan lokacin sai Mussie Kahsay Tesfagergis ya ba ta mamaki bayan da ya kira ta ta wayar tarho, kuma ya shiga jirgin sama daga garin da yake zama a Amurka zuwa Habasha inda mahaifiyar tasa ke zama a yanzu.
Idanun Mussie sun cika da hawaye yayin da ya isa filin jirgin sama domin ya tuna da mahaifiyarsa.
Bayan da aka tambaye shi wace tsaraba ya kawo wa mahaifiyar ta shi, sai ya ce: "Kaina."
An gabatar da mahaifiya da dan nata a wani bikin da iyalansu da kuma tashar EBS suka shirya.
Mussie ya ce ba zai iya tunawa da mahaifiyarsa ba, sai dai ya san fuskarta daga hotunanta da ke wajensa.
Sun rika kuka yayin da suke rungume da juna.
"Na ji dadi da na ga mahaifiyata bayan wadannan shekarun. Wannan ce ranar da nafi yin murna a rayuwata," inji Mussie.
"Zan so in sumbaci samaniya, amma ba zan iya kai gare ta ba. Ina mika godiyata ga dukkan 'yan Habasha," inji mahaifiyarsa.
Dan uwan Mussie, wanda shi ma ya dade ba su hadu ba ya ce: "Ina cike da farin ciki - domin a hoto kawai na taba ganin shi."
Tun da farko dai mahaifin Mussie - wanda dan Eritrea ne, kuma makaniken jiragen sama na yaki ne - ya tafi da shi Asmara, babban birnin kasar tare da 'yan uwansa maza biyu.
Sun bar mahaifiyarsu a shekarar 1966 yayin mulkin Haile Selassie. Zenebech ba ta sake ganin 'ya'yan nata ba.
Sai dai ta taba samun wata wasika - a shekarun mulkin soja na Derg a Habasha - wasikar ta sanar da ita cewa daya daga cikin 'ya'yan nata ya tafi yaki tare da sojojin kungiyar neman 'yanci ta Eritrean People's Liberation Front (EPLF), kuma sauran 'ya'yan nata biyu sun tafi kasashen waje.










