Mutumin da ake kyautata zato ya fi kowa yawan shekaru a duniya ya rasu a Eritrea

Mutumin da ake kyautata zato ya fi kowa yawan shekaru a duniya ya mutu a Eritrea

Asalin hoton, Zere Natabay

Mutumin da ya fi kowa yawan shekaru a Eritrea ya mutu yana da shekara 127 a duniya.

Iyalan Natabay Tinsiew, sun bayyana fatan cewa zai shiga cikin kundin tarihi na duniya Guinness World Records, a matsayin wanda ya fi kowa yawan shekaru a duniya.

Jikansa Zere Natabaym ya shaida wa BBC cewa, irin rayuwar da ya yi ta hakuri da juriya da kuma faran-faran da jama'a inda ya kasance a ko da yaushe yana cikin farin ciki baya bari wani abu ya bata masa rai ita ta ja masa tsawon rai.

Mr Natabay ya mutu salin alin a kauyensa mai suna Azefa wanda yake da yawan mutane 300, sannan kuma tsaunuka duk sun kewaye kauyen.

Jikansa na sa ya ce a cikin takardunsa da suka gano har da na haihuwarsa wanda ya nuna cewa an haife shi a shekarar 1894.

Wani malamin coci da ya shafe shekara bakwai a kauyen, ya ce ko shakka ba bu shekarun Mista Natabay 127, domin yana nan aka yi bikin cikar shekarunsa 120 da haihuwa a shekarar 2014.

Jikan nasa ya ce tuni ya tuntubi wadanda ke da ruwa da tsaki a bangaren tattara bayanai na kundin ababan tarihi na duniya inda aka bukaci ya bayar da dukkan takardunsa na haihuwa da makamantansu, kuma ya bayar, su kawai ya ke jira ya ji daga garesu.

Kundin tarihi na duniyar dai ya dauki bayanan wata 'yar kasar Faransa Jeanne Calment, wadda ta mutu a shekarar 1997 tana da shekara 122, a matsayin wadda ta fi kowa dadewa a duniya.

A shekarar 1934 Mr Natabay ya yi aure, inda matarsa ta mutu a 2019 tana da shekara 99.

A lokacin da yake raye, Mista Natabay ya kasance makiyayi wanda ya ke da garken shanu da na awaki da na kudan zuma.

Jikansa Mr Zere, ya ce za a kasance a ko da yaushe ana tuna kakansa saboda mutum ne mai kirki da kula da jama'a da kuma kokari wajen neman na kansa.