Kane Tanaka: Mai shekara 116 daga Fukuoka a kasar Japan

Bayanan bidiyo, Kane Tanaka, mai shekara 116 daga Fukuoka, Japan.

An haife Kane ne a ranar 2 ga watan Janairun 1903, wato shekarar da 'yan gidan Wright suka tuka jirgi a karon farko.

Kane tana son ilimin lissafi da salon rubutu da ake masa kwalliya.

Masu kula abubuwa da suka shafi kafa bajinta a duniya wato Guinness sun karrama Kane.