Abin da ya kamata ku sani kan shirin zaɓen ƙananan hukumomi a Abuja

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen shugabannin kananan hukumomi shida na yankin babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja a ranar Asabar mai zuwa.
Hukumar zabe ta kasa, wato INEC, ta kulla yarjejeniyar gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali tsakanin jam'iyyun siyasa da za su tsayar da 'yan takararsu a zaɓen.
Wakilan jam'iyyu 14 ne suka sa hannu a yarjejeniyar da 'yan takara 473 da jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Dukkanin bangarorin sun sha alwashin yin aiki da ita, don ganin an yi zaɓen cikin lumana da nasara.
A yankunan kananan hukumomin shida na birnin tarayya Abuja ne za a gudanar da zaɓen a ƙarshen wannan mako.
Honarabul AbdulMalik Ahmed Usman, shugaban jam'iyyar APC na yankin babban birnin tarayya Abuja, ya ce wannan wani mataki ne da aka saba bi, kuma a shirye suke su girmama yarjejeniyar da aka ƙulla.
''Zaman lafiya shi ne komai idan babu shi, ai babu shugabanci, dan haka ya zama dole a gare mu shugabanni mu tabbatar an yi zaben nan cikin zaman lafiya.
Idan mun yi nasara wanda daman abin da muke fata kenan, za mu samu damar yin mulkin cikin kwanciyar hankali, wannan shi ne babban fatanmu.''
Shi kuwa Sunday Dogo Zaka, shugaban babbbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP na yankin babban birnin tarayya Abuja, ya ce hakika sun sa hannu a yarjejeniyar gudanar da zaɓe lami lafiya, amma bisa sharadun hukumar zabe kan yarjejeniyar zaman lafiya.
"Idan INEC su ka sa muka sanya hannu cewa a yi zaɓe cikin zaman lafiya, su tabbatar su ma sun yi adalci idan ba su yi ba, to kuwa ba za mu taba yadda ba ko da kuwa mun sanya hannu a jarjejeniyar zaman lafiya.
Amma a dawo a cuce mu a hana mu magana. Idan an yi zabe mun sanar da magoya bayanmu su tabbatar sun tsaya, an yi komai a kan idonsu.''
Sai dai jami'ar hulda da jama'a ta hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC, Hajiya Zainab Aminu Abubakar ta ce irin wannan yarjejeniya da ake kullawa domin a yi zaɓe cikin zaman lafiya da lumana ne.
Ta kuma shaida cewa matukar aka samu matsalar, to hukumar zaɓe za ta hukunta duk wanda aka samu da karya doka ko tada husuma a lokacin zaɓen.
Wannan zaɓe na kananan hukumomi shida a babban birnin tarayar Najeriya ana ganin wani zakaran gwajin dafi ne, game da babban zaɓen ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.
A wani ɓangaren kuma hukumar zaɓe da jam'iyyun siyasa da kuma jama'ar kasar kwata.











