Fursunonin Liberia: Kurkukun da fursunoni ke fuskantar karancin abinci da kayan sa wa

Prisoner's hands on the bars in his cell door, Liberia - 2011

Asalin hoton, Glenna Gordon/Amnesty International

    • Marubuci, Daga Jonathan Paye-Layleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Monrovia

Lokacin da abinci ya kare wa fursunonin da ke zaman kaso a babban kurkukun babban birnin Liberia a farkon wannan watan, lamarin ya bankado mummunan yanayin da gidajen yarin kasar ke ciki.

Karancin abinci da sauran kayayyakin rayuwa sun shafi dukkan gidajen yari 15 na kasar, matsalar da ta tilasta wa biyunsu daina karbar wasu fursunonin da ake turawa can.

Sai bayan kwana biyu ne wani mai taimakon al'umma da wata kungiya mai taimakon gajiyayyu suka kai daukin kayan abinci, amma sauran matsaloli - kamar cunkoso da karancin kudaden gudanarwa - suna nan ba su kau ba.

A babban gidan yarin Monrovia wanda ke kallon tekun Atlantika, kimanin mutum 1,400 aka dankara a dakunan da aka gina domin mutum 400.

An yi wa gaban gidan yarin kwaskwarima kuma an sanya sababbin kwayayen lantarki, inda masu wucewa na iya zaton komai kalau yake a cikin gidan kamar yadda suke kallonsa daga waje.

Karancin abincin ya ba wata kungiyar fursunonin damar bayyana damuwarsu ga manema labarai wadanda suka halarci bikin bude wani sabon dakin karbar baki da aka gina a kurkukun.

Wani fursunan da ya riga ya shafe shekara uku a kurkuku ya rika yin tsaki yayin da yake bayyana halin karancin abin da za su ci da suke fuskanta.

"Gwamnati na ciyar da mu shinkafa ne sau daya a kowace rana; sau daya a yini," inji shi.

Yayin da yake magana, wasu fursunoni kimanin 12 sun rika girgiza kawunansu, wadda alama ce ta sun amince da abin da yake cewa.

Prisoners on bunk beds in Liberia's Monrovia Central Prison - 2011

Asalin hoton, Glenna Gordon/Amnesty International

Bayanan hoto, Hotunan da aka dauka cikin babban gidan kurkukun Monrovia a 2011 sun bankado irin cunkoson da matsalolin da ke damun mazauna kurkukun

Jami'i mai kula da babban gidan yarin Monrovia, Varney G Lake ya yarda cewa cunkoso a kurkukun "take hakkin bil Adama ne".

Ya kuma koka kan karancin kayayyakin aiki yayin wata hira da yayi da wata jarida mai suna FrontPage Africa.

Lokacin da karancin abincin ya auku, Upjit Singh Sachdeva, wanda wani sanannen dan kasuwa ne da ke zama a Monrovia - wanda dama ya kan taimaka wa gidan yarin da abinci - ya garzaya zuwa kurkukun da kayan agaji.

Mutumin, wanda ka fi sani da sunan "Jeety" ya shaida wa BBC cewa ya kai tallafin nasa ne "domin ya taimaki fusunonin kan hanyar da suke kai ta gyaran halayensu."

Baya ga Mista Jeety, wata kungiya mai suna Prison Advocacy ma ta kai daukin shinkafa da man gyada ga gidan yarin.

Sai dai har wannan lokacin mahukuntan birnin na dogara ga tallafin da ake kai wa ne domin gudanar da gidajen yarin.

A prisoner at Liberia's Monrovia Central Prison eats a bowl of rice - 2011

Asalin hoton, Glenna Gordon/Amnesty International

Bayanan hoto, Kungiyar Amnesty ce ta fara bankado halin da gidajen yarin ke ciki a 2011 bayan da ta wallafa wannan hoton da aka dauka a cikin babban gidan yarin Monrovia

Damar kawo sauye-sauye

A 2011, gwamnati ta fitar da wani tsari na tsawon shekara 10 domin inganta gidajen yarin kasar, kuma Mista Dean ya ce duk da cewa "ana aiwatar da wannan shirin... amma akwai kalubale" ciki har da cewa yawan fursunonin sun kusa ribanyawa sau biyu.

Sannan a kasar da yawancin jama'a ke kwana da yunwa, zai yi wahala jama'a su tausaya wa fursunonin.

Inmates at a ceremony with backs to the camera

Asalin hoton, Jonathan Paye-Layleh/BBC

Bayanan hoto, An yi wa fursunonin da suka yi aikin gina dakin karbar baki kyautar riguna yayin bikin kaddamar da dakin

Wani sabon aikin raya babban gidan yarin Monrovia ya yi amfani da fursunoni wajen gina dakin karbar baki.

Fursunonin sun shaida wa BBC cewa suna so ne su sanar da hukumomi halin da suke ciki domin a kawo sauyi.

Abin da ya rage a yanzu shi ne yadda gwamnatin Liberia za ta magance wannan matsalar, musamman a wannan lokacin da take fuskantar matsananciyar matsalar rashin kudaden shiga.