Masu bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya na zargin gwamnatin Venezuela da aikata laifuka da suka saɓa wa rayuwar bil adama.
Masu binciken sun bayyana cewa gwamnatin ta Venezuela ta aikata laifukan ne a yunƙurinta na daƙile 'yan adawa a ƙasar.
Wani rahoto da aka samu ya nuna yadda gwamnatin ta kashe mutane ba bisa ƙa'ida ba, da ɓatar da mutane da kuma azabtarwa.
Masu binciken sun lissafo sama da manyan jami'an tsaro 40 da ake zarginsu da hannu a aikata laifukan.
Rahoton ya kuma bayyana cewa Shugaban ƙasar Nicolas Maduro da kuma ministansa na cikin gida na sane da laifukan da aka aikatawa, kuma a wani zubin ma, su ne ke bayar da umarnin yin hakan.
Sai dai gwamnatin ta Venezuela ta ce wannan rahoton duk na ƙarya ne.
Za a miƙa rahoton ga Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da haƙƙin bil adama a mako mai zuwa, inda a nan ne Venezuela za ta samu damar mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi mata.