Yakin basasar Ethiopia: Likitoci na daga cikin masu barar abinci a Tigray

Wasu daga cikin malaman jinya da likitoci a asibiti mafi girma a yankin Tigray na Habasha kan roƙi abinci domin su ciyar da kansu kamar yadda ɗaya daga cikin malaman lafiya a ƙasar ya shaida wa BBC.

An shafe watanni takwas ba a biya su albashi ba, wanda hakan ya yi sanadin tilasta musu neman hanyoyin da za su ciyar da iyalansu.

Labari kan halin da likitocin ke ciki na zuwa ne bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa mutane da dama na fama da matsananciyar yunwa a Tigray.

Rahoton ya ce mutum miliyan 2.2 na fama da matsananciyar yunwa.

Rabin mata masu ciki da masu shayarwa na fama da ƙarancin abinci, kamar yadda wani bincike da shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ya bayyana.

Baki ɗaya a Tigray da sauran yankuna biyu da yaƙin ya shafa wato Amhara da Afar, aƙalla mutum miliyan tara ke buƙatar tallafin abinci kamar yadda WFP ya bayyana.

Dakarun tarayyar Habasha na ta yaƙi da ƴan tawaye daga arewacin yankin Tigray tun daga Nuwambar 2020 inda dubban mutane suka rasa muhallansu.

Tsawon lokaci, an rufe hanyoyin Tigray wanda hakan ya sa abu ne mawuyaci a kai agajin kayan asibiti. Haka kuma an rufe bankuna wanda hakan ya sa mutane ba za su iya samun kuɗinsu ba ko su biya wasu.

Likitoci da malaman jinya ba su tsira ba daga wannan wahalar.

Amfani da tufafin sawa a matsayin bandeji

Rabon likitoci da albashi a yankin Tigray tun Mayun bara.

"Akasarinsu sun rage adadin abincin da suke ci a gida. Abinci me mai, kayan lambu da hatsi - farashin ya yi sama wanda ko tunanin saye ba a yi. Wasu sun fara roƙon abinci," in ji likitan.

Ya kuma yi bayani kan yadda ƙarancin kayayyakin lafiya suka kawo cikas ga duba marasa lafiya. A maimakon a luluɓe ciwo da bandeji bayan wanke shi, asibitin Ayder ya dogara ne da tufafin sawa da ake kawowa kyauta inda ake keta su domin wanke ciwo da lulluɓe shi.

BBC dai ta kasa tabbatar da waɗannan batutuwa sakamakon an yanke akasarin hanyoyin sadarwa a Tigray tun bayan da yaƙi ya ɓarke.

Akwai yiwuwar za a samu sauƙi a makon nan, ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta yi ƙoƙarin tayar da jirgi domin kai kayan agaji na lafiya zuwa Mekelle a karon farko tun Satumba.

Babu wasu ayarin motoci ɗauke da abinci da suka kai Tigray tun daga tsakiyar Disamba, sai dai WFP ya ce akwai buƙatar a kai manyan motoci 100 duk rana domin rage yunwa.

Majalisar Ɗinkin Duniya na buƙatar dala miliyan 337 domin ɗaukar nauyin ayyukan agajinta a arewacin Habasha tsawonm wata shida.

Yaƙin Tigray ya ɓarke ne a 2020 bayan Firaiminista Abiy Ahmed ya bayar da umarnin sojoji su kai hari ga dakarun yankin na Tigray a yankin. Ya ce ya yi haka ne domin mayar da martani kan harin da dakarun TPLF suka kai wanbi sansanin sojojin gwamnatin tarayya da dama suke ciki.