An kama mutum 17 da laifin yaɗa bidiyon zolaya da tsorata mutane a Instagram a Iran

Yan sanda a Iran sun kama mutum 17 a kan jerin bidiyon da suka wallafa a shafin Instagram suna zolaya da bai wa mutane tsoro a kan titi.

Masu zolayar sun ɗauki bidiyon kansu ne suna nuna kisan ƙarya tare da jefa kek kan mutanen da ke tafiya a matattakala mai sarrafa kanta, ta yadda ana iya ganin yadda suka razana mutanen da ke wajen.

Yan sanda sun ce masu zolayar na yin hakan ne don samun ƙaruwar mabiya a shafukansu.

Mahukunta a Iran sun ƙara a ido matuƙa kan intanet kuma kamen ya zo ne daidai lokacin da ƴan sanda ke ƙara faɗaɗa yunƙurinsu na daƙile amfani da kafofin sada zumunta.

A wani bidiyo da aka ɗauka a ɓoye, ya nuna wani mutum yana yi wa matsar sa faɗa saboda ta aika wa wani saƙon tes mai alamar soyayya, sannan ya nuna alamar fille mata kai, lamarin da ya tsorata wani ɗan tasi da ke gefe yana kallo.

A wani bidiyon daban an ga wani da abin ya faru ga wani mutum da ke tafiya akan matattakala mai sarrafa kanta da aka jefa da kek a fuska, kafin daga bisani ya fahimci abin da ke faruwa ya bi masu zolayar a guje yana jifansu.

Shugaban yan sandan Tehran ya zargi masu amfani da Instagram da ƙoƙarin tayar da hankulan mutane da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron al'umma. Ya kuma ce an ɗauki bidiyon ba tare da izinin da ya dace ba.

Ɗaya daga cikin masu zolayar da aka kama ya shaida wa masu labarai a Iran cewa ya nemi izinin wadanda ya yi wa abun kafin yaɗa bidiyon, ya kuma ƙara da cewa ya biya su dala 20 a matsayin diyya na duk wata wahala da suka sha.

"Ina son kawai in sa mutane raha ne in kuma bunƙasa shafina na Instagram da mabiya", ya yi bayani.

BBC ta gano cewa wani da shi ma aka kama shi ya amsa laifinsa a wata zantawa da aka yi da shi daga gidan yari. "Da na sani na nemi izini", ya ba da haƙuri.

Yan sanda sun soki masu amfani da shafukan sada zumunta kan abun da ba su sani ba. "Duk masu zolayar 17 da aka kama sun yi karatun gaba da sakandare kuma ma'aikatan kamfanoni masu daraja ne."

Har yanzu babu tabbacin ko an tuhumi waɗanda ake zargin a hukumance, hakan yana nuna za su iya tsira zaman gidan yari.

Kamen ya zo ne daidai lokacin da mahunkunta a Iran ke ƙara faɗaɗa yunƙurinsu na daƙile amfani da kafofin sada zumunta.

A ranar Alhamis ƴan sanda a Tehran sun sanar da ƙara kama mutum 94 a bisa zargin ɓarna da nuna zalunci a shafukan sada zumunta.

A wani lamarin ƴan sanda sun ce sun kama mutum 16 da yaɗa wasu sabbin ɗabi'u marasa kan gado a shafukan sada zumunta, sun kuma ƙara da cewa an rufe shafukan nasu.