Bola Tinubu: 'Mahassada ke cewa tsohon gwamnan Lagos ba shi da lafiyar da zai mulki Najeriya'

Lokacin karatu: Minti 4

Wasu daga masu goyon bayan takarar shugabancin kasar tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu, sun ce mahassada ne ke makƙala masa rashin lafiya don ba sa so ya tsaya takara a 2023.

A ranar Litinin 10 ga watan Janairun 2022 ne Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin Najeriya, lokacin da ya kai ziyara ga Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Amma akwai masu ganin jigon na jam'iyyar APC ba shi da cikakkar lafiyar da ya kamata a ce ya mulki kasar.

Alhaji Ibrahim Masari shi ma kusa ne a jam'iyyar, wanda ya taba zama sakataren walwala na jam'iyar ta APC, kuma daya daga cikin makusantan Bola Tinubu, ya fada wa BBC cewa a ganinsu Tinubu na da cikakkar lafiyar da zai jagoranci Najeriya ba tare da wata matsala ba.

Masari ya buga misali da Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce "in ba ka manta ba da sanin ka ne 'yan jarida aka yi ta yawo da makara ana cewa ai matacce ne ya mutu gobe za a kawo gawarsa jibi za a kawo gawarsa."

"Saboda haka duk wanda ka ji yana cewa wani ba shi da lafiya tsabar hassada ce da jin zafi, mutumin ya tare masa gaba ya rasa yadda zai yi da shi, sai ya ɓata masa suna ko kuma ya karya wa wadanda suke da ra'ayin wannan mutumin gwiwa a nasa tunanin," a cewar Ibahim Masari.

Ya kara da cewa kowa ya ga yadda Tinubu ya taka da kafarsa har wurin shugaban kasa ba tare da an ɗora shi a kan kujera ku an riƙe shi ba.

Saboda haka ya ce batun rashin lafiya ko lafiya "ya rage ruwan masu faɗa su je su yi ta faɗa."

Baya ga batun lafiyar Bola Ahmed Tinubu, wani abu da ke yawo shi ne batun cewa shi Musulmi ne, kuma idan har zai tsaya takara da wahala ya dauki wanda ba Musulmi ba a Arewacin Najeriya.

Hakan na nufin akwai yiwuwar in har jam'iyyar ta tsayar da shi takara, to kuwa ta yiwu za ta tsayar da Musulmi da Musulmi takarar shugaba da mataimakinsa a zaben na 2023.

Yaya za a yi da Osinbajo?

Bugu da kari batun yiwuwar takarar mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da tuni wasu suka fara dasa allunansa ta hadu da cikas, ganin cewa ga ubangidansa a siyasa ya fito.

To amma kan wannan batu na takarar Farfesa Yemi Osinbajo, Ibrahim Masari na ganin cewa a wannan gaɓar ya kamata mataimakin shugaban kasar ya gane cewa "mai wuri ya zo mai tabarma ya nade."

Masu lura da lamuran siyasa suna gani Tinubu zai fuskanci ƙalubale wajen samun tikitin yi wa APC takarar shugaban ƙasa a 2023, musamman ganin yadda shekarunsa suka ja kuma 'yan kasar na fatan ganin an zaɓi mai jini a jika.

Sai dai wasu ƴaƴan jam'iyyar na ganin ya kamata a saka masa da wannan takara ko don irin wahalar da ya yi wa APC da Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓukan 2015 da 2019.

Akwai kyakkyawan zaton cewa APC za ta miƙa wa yankin kudu maso yammacin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2023, don haka ake ganin cewa Tinubu wanda uban gidan Osinbanjo ne a siyasance, a wannan karon zai ɓarje guminsa.

Wasu kuma na ƙishin-ƙishin cewa ba lallai ne wasu gwamnonin jam'iyyar ta APC musamman a arewacin ƙasar su goyi bayan Tinubu ba, yayin da wasu ke ganin cewa ya yi kafuwar da ture shi a jam'iyyar sai an shirya.

Me jam'iyyar APC ta ce?

Sai dai a hannu guda kuma jam'iyyar Tinubun ta APC ta ce babu wanda zai samu takarar jam'iyyar a ɓagas.

Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito hakan daga bakin mataimakin sakataren hulɗa da jama'a na APC Yekini Nabena, a yayin da yake mayar da martani kan maganar Tinubun.

Nabena ya ce, "APC ba za ta bai wa duk wani ɗan takararta tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa a bulus ba; akwai matakai don haka shi (Tinubu) sai ya ci gaba da tuntuɓa.

"APC ba jam'iyyar cin bulus ba ce. Ya kamata ya tuntuɓi har ma sauran waɗanda za su tsaya takarar.

"Don haka a ci gaba da tuntuɓa kuma duk wanda ya yi nasara a zaɓukan fitar da gwani to shi ne zai tsaya takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar a zaɓen 2023."

Wane martanin ƴan Najeriya ke mayarwa?

Wannan batu ya zama shi ne wanda aka fi tattaunawa a kansa a Najeriya tun daga yammacin Litinin har zuwa wayewar garin Talata.

A shafin Tuwita sunan Tinubu na daga cikin waɗanda aka fi yawan ambata har da ƙddamar masa da maudu'i, inda aka yi amfani da shi fiye da sau 25,000.

A Facebook kuwa an ambaci Tinubu tare da neman bayani a kansa sau kusan 90,000.

Da yawa a tuwita sukar wannana niya ta Tinubu suke yi tare da tambayar ko wa zai dauka a matrsayin mataimaki.

A can Facebook din ma duk zancen iri daya be, inda masu suka suka fi yawa, sai dai duk da haka akwai kalina masu nuna goyon baya, sai kuma masu gatse.

A Tuwita, tsohuwar minsitar ilimi a Najeriya kuma ƴar gwagwarmaya Oby Ezekwesili ta rubuta cewa:

"Ƴan ƙasa ne suke da ƙrfin da za su haɗa kai wajen gaya wa mutane irin su Mr Bola Tinubu cewa lokacin yin abin da jagororin siyasa suka saba na "yi ka ba ni" na mulki mara tsari ya wuce a Najeriya Tambayar ita ce, "ko ƴan ƙasa sun shirya haɗa kai wajen tabbatar da hakan?" ✍🏾