Jihar Kano: Hotunan yadda masu baburan A-Daidaita-Sahu suke yin yajin aiki a Kano

Yajin aikin masu A-daidaita sahu a jihar Kanon Najeriya
Bayanan hoto, Yajin aikin masu A-daidaita sahu a jihar Kanon Najeriya

Yajin aikin mako guda da masu baburan A-Daidaita-Sahu a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya suka fara a ranar Litinin 9 ga watan nan na ci gaba da jefa al'ummar jihar cikin mawuyacin hali.

Ɗumbin mutane ne musamman ma mata da ƙananan yara ke ci gaba da taka sayyadarsu zuwa wuraren da suke son zuwa,

Da safiyar Litinin din nan yara yan makaranta sun rika yin tafiya mai nisa zuwa makarantunsu, yayin da mutanen da shekarunsu suka ja wadanda Allah bai hore wa abin hawa ba ke yin tattaki zuwa kasuwa.

Ga wasu hotunan yadda yajin aikin ke kasancewa:

Yajin aikin masu baburan A-daidaita sahu
Bayanan hoto, Yanzu dai ƴar-ƙurƙura ta yi farin jini, domin ta kai ga mutane na cin kwalliya su shiga bodin motar zuwa inda za su je saboda rashin A-Daidaita-Sahu sakamakon yajin aikin da matukansa suke yi
Motocin ƙurƙura kenan suke yawon ɗaukar fasinjoji a ƙasan Gadar Lado da ke ƙwaryar birnin jihar ta Kano

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Motocin ƙurƙura kenan suke yawon ɗaukar fasinjoji a ƙasan wata gada da ke ƙwaryar birnin jihar ta Kano
Suma masu babura masu ƙafa biyu wato ƴan acaɓa kasuwarsu ce ta buɗe duk da haramta goyo a babura da gwamnatin Kano ta yi shekaru da dama da suka gabata
Bayanan hoto, Su ma masu babura masu ƙafa biyu wato ƴan acaɓa kasuwarsu ce ta buɗe duk da haramta goyo a babura da gwamnatin Kano ta yi shekaru da dama da suka gabata
Wasu mutane da ke taka sayyadarsu zuwa wuraren da za su je sakamakon rashin abun hawa
Bayanan hoto, Wasu mutane da ke taka sayyadarsu zuwa wuraren da za su je sakamakon rashin A-Daidaita-Sahu
Wasu yara kenan da ke tafiya makaranta a kekunansu, titu ya yi shiru tsit

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Wasu yara kenan da ke tafiya makaranta a kekunansu, titu ya yi shiru tsit
Yajin aikin ya sanya mutane saɓa dokar hana yin goyo a babura masu ƙafa biyu

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Yajin aikin ya sanya mutane karya dokar hana yin goyo a babura masu ƙafa biyu