Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihar Kano: Hotunan yadda masu baburan A-Daidaita-Sahu suke yin yajin aiki a Kano
Yajin aikin mako guda da masu baburan A-Daidaita-Sahu a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya suka fara a ranar Litinin 9 ga watan nan na ci gaba da jefa al'ummar jihar cikin mawuyacin hali.
Ɗumbin mutane ne musamman ma mata da ƙananan yara ke ci gaba da taka sayyadarsu zuwa wuraren da suke son zuwa,
Da safiyar Litinin din nan yara yan makaranta sun rika yin tafiya mai nisa zuwa makarantunsu, yayin da mutanen da shekarunsu suka ja wadanda Allah bai hore wa abin hawa ba ke yin tattaki zuwa kasuwa.
Ga wasu hotunan yadda yajin aikin ke kasancewa: