Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ke jawo rikici tsakanin 'yan A-Daidaita-Sahu da gwamnatin Kano
An wayi garin Litinin, 10 ga watan Janairun 2022 da yajin aikin direbobin babur mai kafa uku wato A-Daidaita-Sahu a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Hakan na nufin miliyoyin Keke Napep din da ke harkokin sufuri na jigilar fasinja ba za su yi aiki ba daga Litinin a jihar.
An fara yajin aikin ne bayan sanarwar da kungiyar masu baburan ta fitar a ranar Lahadi 9 ga watan Janairun, inda ta roki mambobinta da su kaurace wa tituna har na tsawon mako guda.
Ba wannan ne karo na farko da 'yan A-Daidaita-Sahu ke yajin aikin ba, sai dai mutane da dama na ce-ce-ku-ce kan dalilin da ke jawo hakan.
A bayyane yake cewa akwai ɓaraka tsakanin kungiyar masu baburan da kuma gwamnatin Kano, wanda hakan ce ta jawo irin wannan yaji a bara.
Me yake hada gwamnati da masu A-Daidaita-Sahu?
Masu A-Daidaita-Sahun sun yi zargin cewa ana karbar musu kudade na yin sabuwar lambar da suka yi rijista maimakon biyan kudin sabuntawa.
Kazalika, sun ce ana tatsar su sosai wajen karbar haraji daga naira 100 da suka saba biya yanzu an mayar naira 120 a kowace rana.
Sannan a cewarsu, sun nemi gwamnati ta dauke musu biyan harajin ranakun Lahadi tun da jami'an hukumar Karota ba sa fita aiki a ranar.
Sai dai gwamnatin ta ki jin korafin nasu, inda Karota ke karbar kudin kwana biyu a duk ranar Litinin - har da na Lahadi.
A watan Fabrairun 2021 ma kungiyar direbobin A-Daidaita-Sahu ta yi irin wannan yajin aiki kan batun na'urar da ke gano inda abin hawa yake wato tracker, wadda gwamnati ta ɓullo da shi.
Hukumar Karota ta dage lallai sai masu ababen hawa sun saka na'urar, inda su kuma suka dage cewa ba za su saka ba, a cewar 'yan A-Daidaita-Sahun.
Amma daga baya kungiyoyin fararen hula da na kwadago sun shiga tsakani ta yadda aka samu masalaha.
Me gwamnati ke cewa?
A nata bangaren, gwamnatin Kano ta ce masu A-Daidaita-Sahun ba su da godiyar Allah.
Shugaban Karota Baffa Babba ya ce: "Duk wanda yake Kano kamata ya yi ya gode wa Allah ko don tsaron da jihar ke da shi.
"Su da kansu masu A-Daidaita-Sahun suna ce wa gwamna wannan shekara ce ta afuwa don haka suka roki a rage musu kudaden sabuntawar nan.
''Gwamna ya ce mu je mu sasanta duk matsayar da aka cimma shi kenan. Kudaden harajin nan da su ake samu ake yin wasu hidimomi na biyan ma'aikata albashi a jihar."
Ya ci gaba da cewa "a zagayen da ya yi ranar farko na fara yajin aikin ma a yadda ya ga garin ''ba a ma bukatar hukumar Karota idan babu masu A Daidaita sahun nan.''
Baffa Babba ya ce babu abin da zai sa a fahimci juna tsakanin gwamnati da masu A-Daidaita-Sahu ''ko da cewa aka yi ma su je su ci karensu babu babbaka.''
Sai dai kan korafe-korafe ukun da masu babur din ke yi na biyan kudin na'urar tracker da kudin koriyar lamba da na lambar babur, Baffa ya ce ba haka abin yake ba.
''Tracker, gwamna ya ce a saka wa kowa kyauta saboda tsaro don a dinga gano inda baburan suke, amma duk da an ba su din ma sai suka ki sakawa.
''Na biyu, izini ne da doka ta ce su biya a ba su izinin tuki, su kenan kudin.
''Shi kuwa harajin naira 100 duk wani mai sana'ar tuka abin hawa yana biyan wannan, kuma ba a samun matsala da sauran sai su 'yan A-Daidaita-Sahu."
Ina aka kwana kan yunkurin sasantawa?
Baffa Babba ya ce an roke su kar su je yajin aiki, su bi komai bisa doka amma suka yi biris.
"Abin da ya sa ma muke ba da hakurin yanzu shi ne don ganin wancan karon mun yi kalamai masu zafi, shi ya sa na ce bari mu gwada ba da hakuri kuma a yanzu mu ga ko zai yi rana.
"To ga shi yanzun ma hakurin bai yi rana ba. Da ma wancan karon sai da muka je har kotu kuma kotu ta ce muna kan daidai,'' a cewarsa.
Shugaban Karotan ya ce za su ci gaba da tabbatar da doka da oda a kan duk wani mai abin hawa na haya, ba A-Daidaita-Sahu ba kawai.
''Ni na fita na zagaya kuma na ga wasu da suka dan firfito a yau din ma don yin aikin,'' a cewrsa.
Tasirin yajin aikin
Yajin aikin na yau ya jawo tsaiko sosai don ya sa mutanen jihar shiga wani hali na rashin madafa.
Da yawan fasinjoji suna cikin halin ni-'yasu na rashin abin hawa, saboda A-Daidaita-Sahu ya riga ya zama hanyar sufurin da aka fi amfani da ita a jihar.
Kazalika, yajin aikin wanda aka fara a ranar da makarantu ke budewa bayan hutun karshen zango na farko ya jawo wa dalibai matsala sosai.
Wannan lamari sai da ya jawo har Jami'ar Maitama Sule ta jihar ta sanar da soke jarrabawar da dalibanta za su fara a ranar Litinin din.
"Jami'ar ta soke jarrabawar ne saboda ganin cewa mafi yawan dalibanta A-Daidaita-Sahu ne hanyar sufurin da ke kai su makaranta," a cewar wakilin BBC Hausa a Kano Khalifa Dokaji.
Khalifa ya ce yawanci masu babur mai kafa biyu ne suka bazama tituna a yau don taimakon mutane, wadanda su kuma tuni akwai dokar hana goyo a kansu. Sai dai ya ce babu tabbacin ko taimakon mutane kawai suke yi ko kuma suna karbar kudi.
A hannu guda kuma, masu 'yar karamar A-Kori-Kura ta lodin kaya da aka fi sani da 'Yar Kurkura, su ma sun fita cin kasuwarsu ta lodin mutane a jihar.
Sannan wasu da dama kuma sun ce ba su da wani zabi da ya wuce su taka da kafarsu zuwa duk inda za su je, musamman wuraren ayyukansu, kamar yadda wasu da BBC ta zanta da su suka fada.