Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
ASUU ta gargaɗi gwamnatin Kano kan sayar da filayen Jami'ar Maitama Sule
Kunigayar malaman jami'o'i Najeriya ASUU ta zargi gwamnatin jihar Kano da ƙwacewa tare da sayar da wasu daga cikin ƙadarori mallakar Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar.
ASUU ta ce sayar da wuraren da suke mallakin jami'ar ba komai ba ne illa yunƙurin daƙile ci gaban jami'ar tare da haifar da koma baya a harkokin ilimi a jihar, ta kuma gargaɗi gwamnatin da ta dakatar da hakan.
Sai dai kungiyar ta yi barazanar gurfanar da gwamantin Kano a gaban ƙuliya idan har ba ta dakatar da sayar da filaye mallakar jami'ar ba.
Shugaban kungiyar malaman jami'o'in reshen jami'ar Yusuf Maitama a Kano, Dakta Abdurrazak Ibrahim ya zargi gwamnatin jihar Kano da tashinsu daga cibiyoyin koyarwa guda biyu da suke mallakar jami'ar tare da wasu filayen jami'ar da ke unguwar Tudun Yola da tuni aka fara raba filayen.
"Idan ka duba daga gidan mai zuwa bayan jami'ar za ka ga duka an raba filaye har an fara gine-gine, kuma waɗannan filaye na jami'a ne domin makaranta na da tsare-tsaren da za ta yi da su.
"Hatta cikin matakarantar an shigo ta katanga an fara rabawa, mun ma fara samun labarai cewa an ƙara zuwa da daddare ana aune-aune za a kara ba da filayen.
Ba wai filayen nan kadai ba har da Kwanar Dawaki nan ma an karbe daga hannunmu, an ce ana killace masu korona, amma yanzu kuma babu wasu masu korona da ake ajiyewa a Dawakin.
"Akwai inda muke koyar da sana'o'i inda ake kira Institute of Interprenuership, nan ma an karbe shi da ke Dawakin Tofa an ƙwace an bai wa sojoji," a cewarsa.
Dakta Abdurrazak ya ƙara da cewa "da yawa daga cikin malamanmu sun ce ba su san ana yi ba kuma ba da yawunsu ake yin hakan ba, don haka muke kira ga gwamnati da cewa ya kamata ta dakatar da yin hakan, wadanda ta karbe su ma mu na kiran ta dawo da su," in ji.
Wakilin BBC da ya kewaya domin ganewa idanunsa, ya ruwaito cewa tabbas ya ga an fara gine-ginen da suka kai linta, alamun da hakan ke nuwa shi ne an fara fitar da ginin shaguna, wasu kuma an dasa harsashin ginin.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin shugaban jami'ar Yusuf Maitama Sule, Dakta Mukhtar Kurawa don jin ta bakinsa kan hakan, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.
Amma kwamishinar kula da manyan makarantu ta jihar Kano Hajiya Dakta Mariya Bunkure ta aikawa BBC ta ce ba su da masaniyar cefanar da filayen da ke jami'ar da gwamnatin jihar Kanon ke yi.