Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙungiyar ASUU: 'Ba za mu koma koyarwa ba sai gwamnatin Najeriya ta biya mana buƙatunmu'
Shugaban majalisar dattijai a Nijeriya ya roƙi malaman jami'o'i su janye yajin aikin da suke yi, su koma su buɗe makarantu don ci gaba da karantarwa.
Sanata Ahmed Lawan, ya yi wannan kira ne yayin wani taro da shugabancin ƙungiyar ta ASUU kan batutuwan da suka danganci yarjejeniyar da malaman jami'o'in suka cimma da gwamnatin tarayya.
Tun da farko, Ƙungiyar malaman jami'o'in ta ce ba za ta bi umarnin gwamnati na bude makarantun da suka shafe sama da wata shida a rufe ba.
Farfesa Haruna Musa shi ne shugaban ASUU reshen jami'ar Bayero Kano, kuma a baya-bayan nan ya shaida wa BBC irin buƙatun da ƙungiyar ke son a biya mata kafin komawa bakin aiki.
Farfesan ya ce sun jima suna yarjejeniya da gwamnatin tarayya a kan bukatun da suke son a biya musu, amma kuma shiru.
Ya ce,"Abubuwan da suke cikin yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin, abubuwa ne wadanda idan aka bi su ko shakka babu jami'o'in kasar za su dawo hayyacinsu".
Shugaban kungiyar ta ASUU reshen Jami'ar Bayero Kano, ya ce daga cikin abubuwan akwai;
- Samar da wadatattun kudi wanda za ayi ayyuka domin farfado da jami'oi
- Da biyan alawus na malamai wanda ya taru har ya kai shekara biyar zuwa shida ba a biya ba
- Da matsalar yadda jihohi ke kirkirar jami'o'i barkatai ba tare da yi musu tanadi na wadatattun kudade ba domin tafiyar da su
- Akwai batun samar da wani kwamiti da zai rika ziyartar jami'o'in gwamnatin tarayyar domin ganin irin ayyukan da suke yi don gano nasarori da ma matsaloli da aka samu
- Da kuma batun sabon tsarin biyan albashi na bai daya da gwamnati ta ɓullo da shi na IPPIS wanda shi ma ya zamo matsala babba
Farfesa Haruna Musa, ya ce batun tsarin biyan albashin nan na bai daya wato IPPIS, ya zamo mana wata matsala babba, wadda idan har gwamnati bata yi wani abu a kai ba, to malaman jami'oi ba zasu janye yajin aiki ba.
Ya ce,"Mu aikinmu ba irin na ma'ikata masu zama a ofis bane, mu aikinmu na da tanade-tanade na musamman wanda IPPIS ba zai iya magance su ba".
Malamin jami'ar ya ce shi kansa IPPIS, ya sabawa dokar data kafa jami'oi ta Najeriya ta shekarar 2003.
Ya ce, game da batun wai an biya su wasu kudade, sam ba gaskiya ba ne, domin a yanzu haka malaman jami'a na bin albashi na wata uku zuwa hudu, haka kawai wasu jami'o'in ma da ke bin albashin wata shida zuwa bakwai.