Ba ma son Buhari ya bata lokaci kan karin albashi – ULC

Hadadiyar Kungiyar kwadago ta ULC wato United Labour Congress a Najeriya ta ce ta gamsu da yadda majalisun kasar suka amince da biyan albashi mafi karanci na dubu talatin.

Kungiyar da ke cikin manya-manyan kungiyoyin kwadogon kasar uku mafi girma ta ce fatan ta shi ne shugaban Muhammadu Buhari ya gaggauta rataba hannu saboda dokar karin albashi ta soma aiki a cikin gaggawa.

A jiya Talata, Majalisar dattawan Najeriyar ta amince da naira dubu talatin a matsayin albashi mafi kankanta a kasar.

Kudurin dokar ya yi tanadin cewa albashin zai shafi ma`aikatan gwamnati da kamfanoni masu zaman-kansu.

Tuni dai majalisar wakilan kasar ta zartar da kudurin dokar kwatankwaci wanda majalisar dattawan ta zartar.

Comrade Nasiru Kabir shi ne sakataran tsare-tsare na kungiyar, ya kuma shaida wa BBC cewa wannan babban nasara ce ga demokradiya da ma'aiakatan Najeriya baki daya.

Ya ce yanzu abin da ya saura shi ne ganin dokar ta zama cikakkiyar doka saboda ma'akatan Najeriya su soma cin wannan gajiya.

Comrade Nasir ya ce an jima ana fafutikar kai wa wannan matsayi don haka burinsu shi ne tabbatuwar dokar da kuma ganin cewa babu wanda ya saba dokar.

An dai dade ana kiki-kaka kan albashi mafi karanci da gwamnatoci da kamfanoni za su biya ma'aikatan Najeriya. Sau da dama kungiyoyin kwadago ke shiga yajin aiki a fadin kasar.

Tun a shekarar 2018, majalisar wakilan Najeriya ta sa hannu kan kudirin dokar da ya tanadi a biya naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan gwamnati na jiha da na tarayya.