Ministocin Congo za su karbi albashi muddin rai

Gwamnatin jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ta kare dokar nan da ta ba da damar biyan ministoci albashi da wasu alawus-alawus har tsahon rayuwarsu.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce hakan ba yana nufin nuna fifiko ko son azirtasu ba ne.

Wakilin BBC ya ce mai bai wa shugaban Congo shawara ya bayyana matakin biyansu albashin da tallafa masu kar ku ma su sha wahala bayan sauka daga mukami.

Kudin za su taimaka wajen samun abinci, da lafiya da biyan bukatun yau da kullum.

Karkashin dokar dai tsaffin ministoci za su samu sama da dala 2,000 a kowanne wata, yayin da tsaffin firai ministoci za su samu tagomashin da kuma kula da lafiyarsu a kasashen waje idan bukatar hakan ta taso.

Dokar dai na shan suka, daga 'yan kasar da kusan sama da kashi 50 cikin 100 ke rayuwa cikin bakin talauci.