Bashir Tofa: Tsohon dan takarar shugaban Najeriya ya rasu
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hirarmu da Bashir Tofa:
Rahotanni daga birnin Kano da ke arewacin Najeriya na cewa tsohon dan takarar shugaban Najeriya Alhaji Bashir Othman Tofa ya rasu.
Ya rasu ne da asubahin nan a asibitin Malam Aminu Kano yana da shekara 74 a duniya.
Wasu makusantansa sun tabbatar da cewa tsohon dan siyasar ya yi fama da jinya.
A makon jiya ne aka yi ta watsa labarin da ke cewa Bashir Tofa ya rasu, amma daga bisani aka tabbatar bai rasu ba.
An yi jana'izarsa a gidansa da ke unguwar Gandun Albasa da ke birnin Kano.
Alhaji Bashir Tofa, wanda fitaccen dan kasuwa ne kuma marubuci, ya bar mata da 'ya'ya da dama.
An haife shi a birnin Kano ranar 20 ga watan Yunin 1947 kuma ya yi karatunsa a Najeriya da Ingila.
Marigayin ya tsunduma harkokin siyasa a shekarar 1976 inda ya zama kansila a karamar hukumar Dawakin Tofa a 1977.
Tun daga lokacin ya rike mukamai da dama na siyasa ciki har da Sakataren jam'iyyar rusasshiyar jam'iyyar National Party of Nigeria, NPN reshen jihar Kano.
Bashir Othman Tofa ya tsaya takarar shugaban Najeriya a karkashin rusasshiyar jam'iyyar National Republican Convention, NRC, a zaben da aka gudanar ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 tsakaninsa da marigayi Chief Moshood Kashimawo Olawale Abiola ko MKO Abiola (a takaice) na rusasshiyar jam'iyyar Social Democratic Party, SDP.
Gwamnatin mulkin soji ta Ibrahim Badamasi Babangida ta rushe zaben wanda ya kasance da ce-ce-ku-ce da kuma wasu ke ganin marigayi Abiola ne ya yi nasara, wanda kuma a sanadiyyarsa aka samu ''June 12' wato 12 ga wata Yuni, ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da ita Ranar Dumokuradiyya a Najeriya.
Marigayin, wanda shi ne shugaban kungiyar dattawan jihar Kano, yana cikin dattijan arewacin Najeriya da suka dade suna kokawa kan matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin.
A wata hira da BBC Hausa, ya shaida mana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya daukar shawarar da suke ba shi domin shawo kan matsalar.











