Wata dokar taimaka wa masu son kashe kansu ta fara aiki a Austria

Asalin hoton, Getty Images
Daga ranar Asabar 8 ga Janairun 2022, mutanen da ke da wata cuta ta dindindin ko kuma wadanda cuta ta yi wa lahani za su iya samun taimakon da za su iya kashe kansu.
Majalisar dokokin kasar ce ta amince da dokar a watan Satumba, bayan da kotun kundin tsarin mulki ta yanke hukunci kan batun.
Gwamnati za ta sanya idanu kan wannan lamari, wanda ko wanne mutum da ke son haka sai an samu likitoci sun fara nazari kan lamarin, kuma dole Daya daga cikinsu ya kasance kwararre a fanni bayar d agaji.
Hukumomi sun ce gwamnati ta ware wasu kudade domin samar da wata cibiyar ba da agaji don tabbatar da duk wanda ya zabi mutuwa ba shi da wani zabi sai hakan.
Taimakon za a rika bayar da shi ne ga wadanda suke neman kawo karshen rayuwarsu, kuma hakan ya halarta a makwaciyar kasar Switzerland.
Hakan kuma baya cikin manyan laifuka a mafi yawan kasashen Turai, ciki har da Sifaniya da Belgium da kuma Netherlands.
Duk wani taimako da za a iya bai wa wani mutum domin ya kashe kansa da ba ya cikin wannan tsarin to ya saba ka'ida, kuma dokar ta cire yara da masu tabin hankali daga tsarinta.
Wadanda ke son ganin sun mutu sai sun kawo shaidar asibiti da kuma tabbacin cewa za su iya yanke hukunci a radin kansu.
Bayan kawo shaida daga likitoci biyu, masu son hakan za su yi jiran makonni 12 domin sake Nazari kan hukuncin nasu, amma masu cutar dindindin sati biyu kawai za su jira.
Idan lokacin da aka debe musu ya cika za su iya samun magungunan da ke taimakawa kasha kai, amma sai sun sanar da wani lauya ko wani jami'in ma'aikatar shari'a.











