Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bikin Kirsimeti: Mu’ujuzojin Yesu Almasihu
A ranar Asabar din nan ce Mabiya addinin Kirista suke gudanar da bukukuwan Kirsimeti wadda ake yi kowace ranar 25 ga watan Disamba.
Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Mabiya addinin Kirista a ko ina a fadin duniya na bayyana muhimmancin abubuwan al'ajabi da mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu, wadanda malaman addinin Kirista suke jaddadawa ga mabiyansu a koda yaushe a cikin wa'azi.
Sun kuma yi amanna cewa wadannan mu'ujizoji wata babbar garkuwa ce a rayuwarsu, muddin ba su saba wa abubuwan koyin da ya zo musu da su ba.
Rabaran Joseph John Hayab, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, ya bayyana wa BBC cewa Yesu Isa Almasihu ya zo duniya da abubuwa na ban al'ajabi da kuma abubuwan koyi ga al'ummar duniya.
Rabaran Hayab ya kara da cewa kasancewarsa mai ceton al'umma a duniya wannan ma wani babban abin al'ajabi ne a cikin mu'ujizojinsa da suke alfahari da ita.
"Haihuwar Yesu ta kawo mana ceto, haihuwar Yesu ta kawo mana haske, haihuwar Yesu ta sada mu da Allah," in ji Rabaran Hayab.
"Don haka a kullum idan mun yi maganar Kirsimeti muna ganin ikon Allah ne, kuma shi ne dalilin Kirsimeti.''
Haka shi ma Rabaran Garba Alex Shukau, limamin Cocin Katolika na Saint Loius da ke unguwar Bompai a birnin Kano, ya bayyana wa BBC cewa Yesu Almasihu ya zo duniya tare da abubuwa na al'ajabi da mu'ujizoji da dama, yana mai cewa "mu'ujizarsa ta farko ita ce kasancewarsa mai ceto" ga dan adam.
"Abu na biyu kuma shi ne Yesu Isa Almasihu ya zo duniya domin ya kawo mana salama a cikin zukatanmu, da cikin harkokinmu da juna da 'yan uwa da makwabta har ma da magabata,'' in ji Rabaran Garba.
Har wa yau daya daga cikin mu'ujuzojin Yesu Isa Almasihu in ji Rabaran Hayab ita ce tun lokacin da ya zo duniya babban abin da ya yi shi ne koyarwa a "fannin yafiya, da zamantakewa, da kuma biyayya da umarni."
Rabaran Hayab ya kuma kara da cewa "Abu na uku da Yesu Kiristi ya yi shi ne ya yi abubuwan al'ajabi da yawa - na warkar da marasa lafiya, da na tayar da matattu".
"Don haka idan muka lura da rayuwar Yesu Kiristi sai mu fara da yaya aka haife shi? An haife shi da abubuwan al'ajabi, ya yi rayuwar al'ajabi, kana ya yi mutuwar al'ajabi, ya kuma tashi domin ya tabbatar da abubuwan al'ajabin nan da ya zo ya koyar," a cewarsa.
Haka shi ma Rabaran Garba Alex ya kara jaddada batun warkarwa a matsayin daya daga cikin mu'ujizozin na Yesu Isa Almasihu.
Ya ce:"Lokacin da ya zo duniya ya yi ta warkar da marasa lafiya a yayin da yake yawon wa'azi, marasa lafiya sun samu lafiya, wadanda ba sa gani sun dawo suna gani, wadanda ba sa iya tafiya sun samu iya tafiya."
Wa'azi kan kawo zaman lafiya da salama a tsakanin al'umma na daya daga cikin mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu, a cewar Rabaran Father Garba Alex, wanda yake kokarin wanzar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin al'umma.
"Akwai mu'ujiza a tare da kalaman da yake yi lokacin wa'azinsa, ta yadda yakan ja hankulan mutane zuwa gare shi cikin hikima da nuna kamala, yana bayyana cewa fada da rashin jituwa duka ba zaman rayuwar duniya mai kyau ba ne,'' in ji shi.
Har ila yau malamin addinin Kiristan ya bayyana cewa zuwan Yesu Isa Almasihu duniya da haske wani muhimmin al'amari ne.
A cewarsa "lokacin da ya zo duniya ya haska ta domin littafi mai tsarki ya bayyana mana cewa lokacin da ya zo ya haskaka duniya, da zukatan al'umma."
''Ya zo domin ya zauna tare da mu, ya zo ne domin ya kawo mana haske, haske wanda zai haskaka a cikin rayuwarmu da zukatanmu, da gidajenmu domin ya ba mu zaman salama da zaman ceto."
Malaman addinin Kirista sun kuma bayyana cewa wadanna mu'ujizoji da Yesu Isa Almasihu ya zo da su duniya, wani jigo ne a cikin harkokin rayuwar mabiya addinin a ko ina a fadin duniya.
Rabaran Hayab ya ce don haka yana da matukar muhimmanci mabiya su rika koyi da abubuwan da ya zo da su duniya.
''Ubangiji Allah ya turo shi duniya ne domin ya cece mu daga bata da aikata sabo, da kuma tuba daga zunubai da komawa kan tafarki mai kyau na bin kusanci da Ubangijinmu", in ji shi.
Ga wasu daga cikin mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu:
- Warkar da marasa lafiya
- Hikima cikin wa'azinsa na jan hankali zuwa zaman lafiya da salama
- Kasancewa mai ceton al'umma
- Tayar da matatu ya zuwa rai
- Haske a lokacin zuwansa duniya
- Kamala a cikin kalamansa