'Yadda na fahimci cutar kuturta ce ta kama ni'

Asalin hoton, AFP
An fi alaƙanta ciwon kuturta da gado, amma masana na cewa duk da ana gadar cutar ana kuma daukarta.
Isa (ba sunansa ba kenan) mai shekaru kimanin 50 ya je asibitin Yadakunya da aka fi sani da asibitin Bela da ke birnin Kano domin karbar maganin larurar kuturta.
A shekarar da ta gabata ne Isa ya fara fahimtar sauyi a jikinsa wanda daga baya ya zo asibiti aka kuma sanar da shi cewa cutar kuturta ce.
"Shekara daya kenan na fara jin kasan kafafuna ya yi dundurus musamman ma idan ina yin aiki a cikin ruwa. A bana ne kuma sai na ga kafafun nawa kamar sun kone. Wani lokacin sai ya yi bawo ya bare ya warke da haka amma wani lokacin kuma sai ya gwale har sai na yi jinya."
Isa ya kara da cewa duk da yadda ciwon ke barewa amma "ba ya yi min ciwo sai dai kawai ya bare. Za ka ga ya yi kamar wuta ta kona ni."
Ya ce ba gadon cutar ya yi ba, daga baya ta same shi."Ni duk a iyayena babu mai wannan cuta," in ji shi.
Sai dai ya ce iyayensa da sauran magabatansa sun ba shi shawarar ya yi amfani da maganin gargajiya. "Kuma haka na yi ta amfani da maganin na gargajiya amma ban ga wani sauyi ba."

A yanzu dai haka jihar ta Kano ta samu mutum 118 da ke fama da cutar kuturta, abin da ke nuna cewa a kan samu mutum daya a duk cikin 10,000 da ke samun wannan cuta.
"Wannan ya nuna har yanzu ana samun masu ɗauke da wannan cuta jifa-jifa kuma dole ne a sa ido domin ganin ba ta samu wurin zama ba," in ji Dr Ibrahim Aliyu Umar, jami'i mai kula da sashen dakile cutar tarin fuka da ta kuturta a Kano.
Galadiman kutaren Bela da ke Kano, Bala Adamu ya ce rashin ilimi da wayewa na daga cikin dalilan da ya sa aka sami dawowar cutar ta kuturta a tsakanin al'umma.
"Mutane suna boye cutar saboda tsabar gidadanci domin kada a ce suna da cutar kuturta."
Da ma dai wani rahoton Hukumar yaki da cututuka masu yaduwa a Najeriya na 2018 ya nuna cewar kimanin mutum dubu 3,500 ne suke kamuwa da cutar kuturta a kasar.
Hakan ya nuna cewar an sami karin masu fama da wannan cuta bayan shekaru 20 da hukumokin Najeriyar suka ce an magance ta a kasar baki daya.











