Amfanin ganyen tazargade ga lafiyar ɗan adam

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
Kasar Madagascar ta ja hankalin duniya a watan Afrilu lokacin da ta sanar cewa tana yin amfani da wani ganyen tazargade domin maganin cutar korona.
Shugaban kasar Andry Rajoelina ya rika tallata ganyen tazargade mai dauke da sinadarin artemisia a matsayin maganin korona.
Kasashen Afirka da dama ciki har da Najeriya sun karbi maganin domin gwada shi kan masu fama da cutar korona.
Babu wata shaida da ke nuna cewa ganyen - wanda yake maganin zazzabin ciwon sauro - zai iya warkar da Covid-19, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Me ye asalin maganin Madagascar?
Masana tsirrai sun ce maganin ya samo asali ne daga wani tsiro da ake hada maganin maleriya, wanda a turance ake kira Artemisia annua, wanda dangi ne na tazargade da Hausawa suka sani.

Asalin hoton, Getty Images
Malam Umar Suleiman mai karatun digiri na uku a fannin magungunan da akan samu daga bishiyoyi da dabbobi da ma'adinai, a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya ya ce bishiyar ta samo asali ne daga China wacce ake amfani da ita wajen hada maganin maleriya na ACT.
Ya ce tun 1972 aka gano cewa ganyen bishiyar yana dauke da sinadarin da yake kawar da zazzabin maleriya.
Amma ya bambanta da ganyen tazargade da ake kira Artemisia Absinthium.
Dalilin tabbatar da ingancin maganin

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu lalube ake ba a gano magani ko riga-kafin cutar korona ba. Akwai bincike da ake a kasashe da dama domin samar da maganin cutar.
Ko da yake sama da mutum miliyan 28 ne suka kamu da cutar a duniya amma kuma ana warkewa daga cutar idan an kiyaye wasu ɗabi'u na inganta garkuwar jiki da shawarwarin likita.
"Kusan kashi 90 na waɗanda suka kamu da korona suna warkewa, domin kana iya cin wasu abubuwa ko yawan shan ruwa kuma ka warke," kamar yadda Dr Sani Aliyu babban jami'i a kwamitin shugaban ƙasa kan yaƙi da korona a Najeriya ya shaida wa BBC.
Sai dai Dr Muhammad Ibrahim Jawa shugaban wata makarantar koyar da kimiyar maganin gargajiya ta Afirka a Najeriya da ke Damaturu a jihar Yobe ya ce ma'aunin tabbatar da ingancin maganin gargajiya ba daidai yake da maganin bature ba. Kuma ba ma'aunin bature mutane suke amfani da shi a Afirka ba, domin tafiyarsu ba daidai ba.
"A maganin gargajiya ba sinadari ba ne domin ba mu da ma'aunin sinadarin da ke cikin itace amma ɗabi'ar ce da za a gano ko maganin da za a iya sha ne ko na shaƙa ko turarawa.
Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai shugaban sashen binciken magunguna a Jami'ar Bayero Kano, ya ce maganin gardajiya na Madagascar abu ne wanda ake ganin ci gaba ne wanda idan aka tabbatar da ingancinsa zai taimaka wa mutane da dama.
Sai dai ya ce binciken tabbatar da ingancin magani yana ɗaukar lokaci, watakila har cutar ta wuce ba a kamamala binciken ba.
"Matakan da ake bi na gwajin magani domin tabbatar da ingancinsa ana ɗaukar lokaci, domin sai an gwada da dabbobi kafin a dawo kan mutane. Za a iya ɗaukar watanni ko shekaru kafin tabbatar da ingancin maganin."
Ya kuma ce ko wane mai magani yana son kare maganinsa, don ba ya son kowa ya san yadda maganin yake domin a ɗinga amfani da shi yadda aka ga dama.
"Don haka Madagascar ba za ta so Najeriya ta yi binciken ƙwaƙwaf ba domin gano abin da maganin ya kunsa ba," in ji shi.
Shin Tazargade ne da Hausawa suka sani?

Asalin hoton, Getty Images
Umar Sulaiman, mai karatun digiri na uku a fannin magungunan da akan samu daga bishiyoyi da dabbobi da ma'adinai, a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya ya ce bishiyar tana da bambanci da tazargade ta fuskar sinadaran da suke ɗauke da su amma dukansu dangi ɗaya ne.
Ya ce ba lalle ba ne sinadaran da ke cikin tazargaden da Hausawa suka sani a same su a ganyen da Madagascar ta ce yana maganin korona.
Sai dai Dr Muhammad Ibrahim ya ce dukkaninsu tazargade ne amma sukan bambanta daga yanki zuwa yanki da kuma ɗabi'unsu.
Ya ce ya taɓa zuwa bincike Madagascar lokacin da yake karatun digirisa na uku kuma har ya taɓa zuwa da samfurin ganyen bishiyar Madagascar.
"Dukkaninsu tazargade ne, amma sun banbamta ne saboda yanayin kasa da kuma sinadaran da suke ɗauke da su."
"Idan har za a yi noman tazargade a Nijar da kuma Najeriya za a samu bambanci saboda yanayin bambancin ƙasa."
"Idan da za a yi noman tazargade a kudancin Najeriya, to zai iya bambanta da wanda aka noma a arewaci," in ji Dr Jawa.
Cutukan da Hausawa ke amfani da Tazargade

Asalin hoton, Getty Images
Aliyu Muhammad Dan Hausa, masanin magungunan gargajiya kuma marubucin "Hausa Mai Dubun Hikima" da 'Kundin Magani" na itatuwa da tsirrai 1111 na haɗin guiwa da Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce Tazargade da yawa Hausawa na mafani da shi wajen magance cutuka bambanta.
Masanin ya ce ana amfani da tazargade wajen magance kamar matsalolin da suka shafi dattin ciki, kumburi da ƙugi na ciki.
Ana hada tazargade da kamar gauta da tsamiya domin maganin ciwon ciki. Ana kuma jiƙa shi a ajiye idan ya jiƙu duk lokacin da aka ci abinci a sha.
Ya kuma ce Hausawa na amfani da shi domin inganta garkuwan jiki.
Sannan a Bahaushiyar al'ada, Hausawa sun yadda da maita da camfi da shedanun boye. Bahaushe ya yadda idan yana shan tazargade yana da wahala wani shedani ya kama shi ta hanyar maita ko wata hanya ta daban.
Dan Hausa ya ce ana amfani da tazargade wajen magance cutuka da ke hana wa mutum rashin samun isasshen bacci ko wasu al'amurra na damuwa ko miyagun mafarkai.











