Black Axe: Kungiyar asiri da ta yi dumu-dumu a harkokin siyasar Najeriya

Wata kungiyar asiri mai hadarin gaske, wadda aka alakanta da kashe-kashen da ake yi a Najeriya, ta yi dumu-dumu cikin harkokin siyasar kasar.
Sannan ta shiga harkokin halasta kudaden haram, da hada-hadar kudade ba a kasar kadai ba har da kasashen wajen, kamar yadda dubban takardun bayanai da bahasin wadanda BBC ta zanta da su suka bayyana.
Shekara da shekaru kenan da kungiyar asiri ta 'Black Axe' ke gudanar da ayyukanta, kuma tana daga cikin wadanda ake matukar tsoro a kasar.
Shiga cikin irin wadannan kungiyoyi dai a kasar haramtacciyar mu'amala ce a dokokin Najeriya.
Sashen binciken kwakwaf na BBC Africa Eye, ya shafe shekaru biyu yana bibiyar ayyukan kungiyar Black Axe, tare da tattaunawa da tsofaffin 'yan kungiyar, da nazarin dubban takardun bayanai da wasu daga cikin mambobinta suka sace.
Abu ne mai matukar wuya a iya nazarin baki dayan takardun, amma duk da hakan BBC ta yi cikakken nazari da tantance wasu daga ciki.
Cikin abin da muka tsakuro, akwai sakonnin imel na wani fitaccen dan kasuwa da ya kuma tsaya takara a zaben shekarar 2019 dan jam'iyyar APC mai mulki mai suna Augustus Bemigho da hakan ya nuna dan kungiyar Black Axe ne, yana da hannu a damfarar miliyoyin daloli ta intanet.
Kundin mai shafi 18,000 da aka tattaro na sakonnin imel masu alaka da Mista Bemigho, sun hada da sakon da ke nuna ya aike wa abokan huldarsa yadda za su yi damfara ta intanet har sau 62, ta kuma yin magana da wadanda ake son damfarar.
"Mun cire kusan dala miliyan 1 daga gare shi," in ji wani sakon imel da Mista Mr Bemigho ya aike, da ke nuna ana magana ne a kan wani mutum.
Cikin sakon an rubuta cikakken sunan mutumin da adireshinsa da lambar tarho, da cikakken bayanin yadda za a damfare shi.
BBC ta bibiyi biyu daga cikin wadanda aka damfara daga sakonnin imel Mista Bemigho, wadanda aka damfara akalla dala miliyan 3 da dubu 300.
Wata kungiya da ke sa ido kan damfara ta duniya ta ce kudaden da kungiyar Black Axe ke samu ka iya kai wa biliyoyin daloli daga damfarar da ake sanyawa su na yi.
Ko da BBC ta tuntubi Mista Bemigho kan wadannan zarge-zarge bai ce uffan ba.
Wasu daga cikin bayanan da aka samu, sun nuna munanan ayyukan kungiyar da ba za su wallafu ba.
Sai dai kididdiga ta nuna ayyukan da kungiyar ta yi tsakanin shekarar 2009 zuwa 2019, masu tashin hankali ciki har da hannu a siyasar kasar musamman a jihar Edo.
Bayanai biyu sun nuna sun yi hada-hadar kudi da suka kai naira miliyan 35 a birnin Benin, inda aka tura wani kamfani mai suna Neo-Black Movement of Africa (NBM) wanda masu sa ido ke cewa yana da alaka da kungiyar asirin, da nufin duk yadda za a yi a kawo kujerar gwamnan jihar a zaben 2012.
Su ma a madadin tukwici an bai wa kamfanin NBM reshen Benin ayyuka 80, wanda kuma gwamnati ta bayar da su.
Wani mai fafutuka a Benin Kurtis Ogebebor, wanda yake kokarin hanawa da wayar da kan matasa kaucewa shiga kungiyar Black Axe, ya shaida wa BBC cewa siyasar Najeriya ta koma wata kungiyar ''Mafia''.
"Ayyukan kungiyar asiri sun mamaye harkokin gwamnati, daga sama har kasa". "Za ka same su a ko'ina."

Kamfanin Neo Black Movement of Africa ya musanta alaka da kungiyar Black Axe, kuma lauyan kungiyar ya shaida wa BBC cewa an kori duk wani da aka samu mamban kungiyar Black Axe ba tare da bata lokaci ba.
Kuma NBM ta yi ikirarin suna da mambobi miliyan 300 a sassa daban-daban na duniya, yawanci suna ayyuka ne a kungiyoyin agaji, da ba da tallafi a gidajen marayu, da makarantu da 'yan sanda a cikin Najeriya da kasashe makwabta.
"NBM ba ta da alaka da Black Axe. NBM ba ta da alaka da bata-gari," in ji Ese Kakor, shugaban NBM, a hira da BBC.
Sai dai kungiyoyin da ke sa ido na kasa da kasa sun yi bayanin kan yadda suke kallon NBM. Ma'aikatar cikin gida a Amurka ta ayyana NBM a matsayin kungiyar masu aikata muggan laifuka, sannan sun ce wani bangare ne na "kungiyar asiri ta Black Axe", sannan hukumomin kasar Canada sun ce kungiyar Black Axe da NBM "duka daya suke".
A watannin da suka gabata, hukumomin tsaron hadin gwiwa, kamar hukumar ta Amurka, hukumar tsaro ta FBI da 'yan sandan kasa da kasa, sun sanya wa Black Axe ido lamarin da ya kai ga mambobin NBM 35 a kasashen Amurka, da Afirka ta Kudu kan laifuka masu alaka da cuwa-cuwar miliyoyin daloli ta intanet.
Kuma NBM ta shaida wa BBC cewa tun daga lokacin aka kori mutanen.
A shekarar 2017, hukumomin kasar Canada sun wargaza wata wata kungiya da ke satar kudade ta intanet, da kuma hannun Black Axe da ta kai dala biliyan 5, wanda hakan ya nuna irin karfin da kungiyar ta yi a duniya.
Babu wanda ya san akwai shiri irin hakan, amma takardun da aka kwarmata sun nuna mambobin kungiyar na tattaunawa da juna daga Birnin Lagos na Najeriya, da Landan na Birtaniya, da Tokyo na Japan, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da gwamman kasashe.
A Najeriya, Black Axe ta yi fice wajen aikata muggan laifuka a itituna da cin zarafin mutane da zargin yamutsa siyasa da kasuwanci a kasar. Sai dai harkokinsu sun wuce duk yadda akai tsammani.
Tsohon mamba a gwamnatin jihar Edo, a karon farko ya yi hira da kafar yada labaran kasar waje, ya kuma shaidawa BBC mmbobin Black Axe na cike makil a madafun iko.
"Idan ka zaunar da ni ka tambaye ni, in nuna maka mabobin kungiyar asiri ta Black Axe a cikin ma'aikatan gwamnati, zan nuna maka su," in ji Tony Kabaka, wanda ya fadawa BBC ya tsallake rijiya da baya na yunkurin hallaka shi, tun bayan barin aikin gwamnati, wanda kuma harsashan bindiga suka yi wa babbar kofar shiga gidansa da katangar kwalliya.
"Kusan yawancin 'yan siyasa na ciki, kai kusan kowa ma na cikinta," in ji shi.
Mun aika wa gwamnatin jihar Edo sako domin kare kansu kan zarge-zargen alaka da kungiyar asiri ta Black Axe, amma ba su ce uffan ba.











