Adama Barrow ya yi nasara a zaben shugaban kasar Gambia

Asalin hoton, Reuters
Hukumar zabe mai zaman kanta a Gambia ta sanar da Shugaba Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar a ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar zaben kasar Gambia ta fitar ya nuna cewa, Mista Barrow ya samu kuri'u kusan sau biyu fiye da wanda babban abokin hamayyarsa Ousainou Darboe ya samu (53% zuwa 28%).
Adamu Baro ya lashe kuri'u 457,519 yayin da dan takarar jam'iyyar adawa Ousainou Darbor ya samu kuri'u 238,253.
'Yan takarar 'yan hammaya uku a Gambia sun yi watsi da sakamakon zaben da ya nuna cewa Adama Barrow ne ke kan gaba.
Tun farko sakamako daga gundumomi hamsin daga cikin gundumomin 53 na kasar sun bai wa shugaba Barrow damar jagoranci
Sai dai babban mai kalubalantarsa, Ousainou Darboe, da wasu 'yan takara biyu sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka nuna rashin amincewa da alkaluman.
Ousainou Darboe, da wasu 'yan takara biyu sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka nuna rashin amincewa da alkaluman.
Sun ce an fuskanci jinkiri wajan sanar da sakamakon karshe na zaben kuma sun yi ikirarin cewa wakilan jam'iyyunsu ba su amince da sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta sanar ba.
Sun kuma yi zargin cewa an samu matsaloli a wasu rumfunan zabe amma ba su bayar da cikakken bayani ba.
Shugaba Adama Barrow ya hau kan karagar mulki shekaru biyar da suka gabata wanda ya kawo karshen mulkin Yahya Jammeh fiye da shekaru ashirin.
Tsohon sojan dai yana gudun hijira a Equatorial Guinea bayan ya ki amincewa da shan kaye da ya sha.
Sai dai tasirinsa da goyon bayansa ba za su iya kawar da sakamakon zaben da aka yi a baya ba, inda ya goyi bayan dan takarar jam'iyyar adawa Mamma Kandaeh.
Wakilin BBC a Banjul, babban birnin kasar, ya ce magoya bayan shugaban kasar sun fara murna, yayin da dubban magoya bayan Mr Darboe suka taru a gidansa.
Akwai tsauraran matakan tsaro a ofishin hukumar zaben. Ana kallon zaben a matsayin wani gwaji na ci gaban dimokuradiyyar Gambiya, shekaru shida bayan da Mista Barrow ya doke tsohon sojan kasar Yahya Jammeh.

Ana sa ran shugaba Barrow zai magance matsalar rashin aikin yi da tsadar rayuwa da kuma inganta fannin yawon bude ido da cutar Corona ta shafa.
Zaben dai wani gwaji ne na ci gaban dimokradiyyar Gambia bayan zamanin Jammeh.
Yan takara shidda ne suka tsaya takarar zaben shugaban kasa ciki harda shugaba Adama Barrow.










