Abin da ya sa 'yan Gambiya suke kaɗa ƙuri'a da duwatsu

Asalin hoton, AFP
A jerin wasikun da 'yan jaridar Afirka ke aiko mana, marubuci dan Saliyo da Gambia, Ade Daramy ya ce cikin shekaru biyar 'yan Gambia sun ga sauyin siyasa iri daban-daban, sai dai salon yadda suke kada kuri'ar zaben shugabanni bai sauya ba ko kadan.

Yawancin 'yan kasar na alfahari da salon yadda suke kaɗa ƙuri'a da ya bambanta da na sauran ƙasashe.
Idan suka je rumfunan zaɓe a ranar 4 ga watan nan, domin zaɓar shugaban kasa ba za a yi amfani da takardun kaɗa ƙuri'ar ba.
Maimakon hakan, da zarar sun isa rumfar zaɓe, bayan an kammala tantance su, za a nuna wa mai kaɗa ƙuri'a wani duro da aka yi wa fenti da alamar jam'iyyun siyasar ƙasar da ƴan takara.
Saman duro ɗin a rufe yake ruf, sai wani ƙaramin bututu da aka sa a sama, inda a nan jami'an hukumar zaɓe za su bai wa kowanne mai kaɗa ƙuri'a wani farin dutse mai garai-garai da zai jefa ta bututun da ke sama ga dan takarar da yake son zaɓa.

Asalin hoton, AFP
Da zarar dutsen ya fada ciki zai yi ƙara, a nan ne jami'ai za su gane ko wani ya yi ƙoƙarin kada ƙuri'a sau biyu.
Da zarar an rufe rumfunan zabe, za a ƙidaya duwatsun da ke cikin kowanne duro sannan a rubuta a jikin takardar da ke dauke da hoton dan takara da jam'iyyarsa.
A shekarar 1967 bayan samun 'yancin kan Gambia, aka fito da wannan salon zaben saboda yawan jahilai a kasar a wancan lokacin.
An yi gagaruman sauye-sauye bayan shan kayen da Yayha Jammeh ya yi a zaben shugaban kasa a shekarar 2016.
Kaucewa hadarin dare
Wasu daga cikin jami'an hukumar zabe na fatan daya daga cikin hanyar kauce wa hadarin dare da ake kauce wa shi ne zaɓe da duwatsu.
Sun kafe cewa tun da an sake buɗe kafar dimokuradiyya a kasar, akwai yiwuwar samun karin ƴan takara a zabuka na gaba, yayin da duro da duwatsu ka iya sauyawa nan gaba.
A baya duro uku ne kadai ake girkewa a kowacce rumfar zaɓe.
Amma lokacin mulkin Mista Jammeh na shekara 22, ba a samun 'yan takarar shugaban ƙasa masu yawa.
Haƙiƙanin gaskiya ma, shugabannin kasa uku kadai Gambia ta taɓa yi.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 1994 ne Mista Jammeh ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da mulkin Shugaba Dawda Jawara.
Yawancin masu sa ido na da yaƙinin zaɓen shekarar 1996 ne kaɗai Mista Jammeh ya lashe ba tare da maguɗi ba, a lokacin da ba a dade da yin juyin mulkin ba sannan bai fara shimfida salon mulkinsa ba.
Sun ce sauran zaɓukan da suka biyo baya, shi kadai ke yin nasara, sannan shan kaye a zaben shekarar 2016 da Adama Barrow ya yi nasara, ya zo masa da mamaki.
Zaben an yi shi ne tsakanin 'yan takara biyu, Jammeh da Barrow wanda gamayyar jam'iyyu da kungiyoyin 'yan hamayya suka tsaida, yayin da ɗaya ɗan takara Mama Kandeh ya yi nasara da kashi 17 cikin dari na ƙuri'un da aka kaɗa.
Shugaba Barrow yana neman wa'adin mulki na biyu, amma a wannan karon karkashin sabuwar jam'iyyar da ya kafa.
A karon farko alamu sun nuna zai fafata da 'yan takara 22, lamarin da ya sanya hukumar zabe za ta tanadi duro da duwatsun kaɗa ƙuri'a masu yawa, hakan ya nuna babu wani dan siyasa da zai sauya tsarin a halin yanzu.
Sai dai daga bisani, 'yan takarar suka yi ta zillewa har aka bar mutum 6 kacal, amma duk da hakan suna da yawa a kasar mai yawan al'umma sama da miliyan 2.
Har yanzu Jammeh na raba kawunan 'yan kasa
Yawan 'yan takarar da suka fito, ya nuna gagarumin sauyin da aka samu a siyasar Gambia.
A lokutan baya, ba a samun wadanda suke fitowa takara, ko dai suna jin tsoron karawa da Mista Jammeh, ko ba sa son bata wa kansu lokaci domin ba za su yi wata nasara ba.

Amma a dan tsakanin nan, a abin da ake kira "Sabuwar Gambia", wannan tsoron ya kau, an kuma samu 'yancin fadar albarkacin baki.
Wani lamari da ba a taba gani ba, kuma shekaru biyar da suka gabata idan aka ce hakan za ta faru a Gambia, babu mai amincewa, shi ne fitowar mai wasan barkwanci da ake kira Wagan, da ke gabatar da shirin talabijin a kowanne mako, inda a ciki yake fitowa gaba-gadi yana barkwanci kan 'yan siyasa ciki har da shugaban kasa
'Yan jarida na gudanar da aikinsu ba tare da tsangwama ba ko tsoro, ko azabtarwa ko kisa da sace mutane kamar a lokacin mulkin Yahya Jammeh.
Duk wadannan abubuwan da aka aikata sun fito fili a lokacin kaddamar da Kwamitin Fadar Gaskiya da ya saurari bahasin kusan mutum 400 daga watan Janairun shekarar 2019 zuwa Mayun 2021.
A makon da ya wuce ne kwamitin ya wallafa rahoto har kashi 17, an kuma bai wa shugaban kasa watanni shida ya yi nazari da daukar mataki.

Asalin hoton, AFP
Hakan na nufin duk wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa da za a yi ranar 4 ga watan nan, shi ne zai yi nazari kan rahoton a kuma lokacinsa ne za a san matakin dukkan azabar da Mista Jammeh ya yi wa mutanen.
Duk da cewa yan gudun hijira a Equatorial Guinea, tsohon shugaban na kokarin katsa-landan a zaben da ke tafe.

Wasu wasikun daga Afirka:

Tsohon shugaban mai shekara 56 na ci gaba da raba kawunan 'yan kasar, duk da cewa jam'iyyarsa ta APRC, wadda daman shi ya kafa ta, ta yi faduwar bakar tasa a zaben da ya sha kaye,
Amma kawai, sai jam'iyyar ta shiga kawancen jam'iyyar shugaba Adama Barrow, lamarin da ya bata wa Jammeh rai wanda ya dinga aikewa da sakon muryar nuna goyon baya ga Mr Kandeh.
An yi ta sanya muryar a wuraren gangamin yakin neman zaben Mista Kandeh. Sai dai babbar matsalar da ke bibiyar Gambia kamar wasu kasashen duniya ita ce annobar korona.
Kasar mai tsuburai da teku masu ban sha'awa, ta dogara ne da fannin yawon bude ido wajen samun kudade amma annobar korona ta hana wannan. Ma'aikata sun rasa ayyukan yi.

Asalin hoton, AFP
Ko kafin annobar korona, 'yan kasar na kokarin tsallakawa nahiyar Turai sakamakon karancin ayyukan yi da kasar ke fama da shi.
Ko ma waye ya yi nasara a zaben 4 ga watan nan, bunkasa kasar, da samar da ayyukan yi da ababen more rayuwa, da bullo da sabbin dabarun da za su ja hankalin masu yawon bude ido shi ne babban aikin da ke gabansa.

'Yan takarar da za su fafata:
- Shugaba mai ci Adama Barrow (na jam'iyyar National People's Party)
- Ousainou Darboe (na jam'iyyar United Democratic Party) - Lauya wanda ya yi aiki da shugaba Barrow na takaitaccen lokaci a matsayin mataimakin shugaban kasa. Yana daga cikin kawancen da ya hambarar da mulkin Jammeh, kuma karo na biyar kenan yana tsayawa takara.
- Essa Mbye Faal (na jam'iyyar Independent) - Lauya kuma tsohon shugaban kwamitin jin bahasi kan muggan laifukan da aka aikata a tsahon mulkin Jammeh. Yana takara a karon farko.
- Mama Kandeh (na jam'iyyar Gambia Democratic Congress) -Shi ya zo na uku a zaben shekarar 2016
- Abdoulie Ebrima Jammeh (na jam'iyyar National Unity Party) - tsohon malamin makaranta, wanda ya taba rike mukamin shugaban hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Gambiya. Yana takara a karon farko
- Halifa Sallah (na jam'iyyar People's Democratic Organisation for Independence and Socialism) - dan majalisa da ke neman kujerar shugaban kasa a karo na biyar












