Cristiano Ronaldo: Dan wasan Man Utd da Portugal ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo 800

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko a tarihi da ya ci ƙwallo 800 a mataki na ƙwararru bayan ya ci ƙwallo biyu a wasan da Manchester United ta doke Arsenal 3-2 z ranar Alhamis.
Ronaldo yanzu na da yawan ƙwallo 801 a wasa 1,097.
Yanzu Ronaldo ya ci ƙwallo 130 a karo biyu da yake bugawa Manchester United wasa, da ƙwallo biyar da ya ci wa Sporting Lisbon da 450 da ya ci wa Real Madrid da 101 da ya ci wa Juventus da kuma 115 da ya ci wa Portugal.
Shi ya fi cin kwallo a gasar zakarun Turai da kuma Real Madrid.
Shin Ronaldo ne ya fi kowa yawan cin ƙwallo a tarihi
Babu wasu alƙalumma da aka tattara da ke nuna wanda ya fi yawan jefa ƙwallo a raga, amma Ronaldo ne yanzu kan gaba a wasanni da aka yi a hukumance a mataki na ƙwararru.
Hukumar ƙwallo ta Jamhuriyyar Czech ta ce Josef Bican da ya taka leda Czechoslovakia da Austria ya ci ƙwallo 821 a wasanni a hukumance. A wani wurin an bayyana jimillar ƙwallayensa 805, amma waɗannan sun ƙunshi ƙwallayen da ya ci a wasannin da ba hukumance ba.
Fitaccen ɗan wasan Brazil Pele da Romario dukkaninsu sun yi iƙirarin cin ƙwallo 1,000 amma bayan cire wasanni na sada zumunci alƙalumman sun sauka zuwa 700.
Wasu alƙalumma da ba na hukuma ba na RSSSF sun ce Pele ya ci ƙwallo 769, Romario da Ferenc Puskas dukanninsu sun ci ƙwallo 761, waɗanda suka yi kusa da Ronaldo a mataki na ƙwararru
Lionel Messi ne ke bi masu wanda ya yawan ƙwallo 756, Argentina (80), Barcelona (672) da Paris St-Germain (huɗu).











