Kofin duniya ne ya rage wa Lionel Messi da bai ci ba

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Litinin Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2021 wato Ballon d'Or.

Da wannan sakamakon kyaftin din tawagar Argentina ya lashe Ballon d'Or karo na bakwai kenan jumulla, shi ne kan gaba a yawan lashe kyautar, bayan da Cristiano Ronaldo ya ci karo biyar.

Yanzu dai kofin duniya ne ya rage da Messi bai lashe ba a tarihin sana'arsa ta tamaula a duniya, bayan da ya karbi kyautuka da dama a kungiya da kuma a tawagar Argentina.

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Kyaftin din Argentina ya fara zuwa gasar cin kofin duniya tare da babbar tawagar kasar a 2006, wanda ya buga karawa uku da cin kwallo daya ya bayar da daya aka zuwa a raga.

Ya sake halartar gasar a karo na biyu a 2010 da ya yi wasa biyar da bayar da kwallo daya aka zura a raga.

Haka kuma Messi ya je gasar cin kofin duniya a 2014, inda ya yi karawa bakwai da cin kwallo hudu da bayar da daya aka zura a raga, ya kuma halarci wadda aka yi a Rasha, wanda ya ci kwallo daya ya bayar da biyu aka zura a raga.

Argentina ta kai karawar karshe a gasar da Brazil ta kai karbi bakunci, wanda Jamus ta lashe kofin.

Messi wanda ya lashe Copa America a bana ya ci kwallo shida a gasar kofin duniya da cin daya a 2006 da zura hudu a raga Argentina ta kai karawar karshe a 2014, wanda ya lashe takalmin zinare a gasar da zura daya a raga a gasar 2018 - ya kuma ci 34 a wasannin sada zumunta.

Kyautukan da ya lashe a Barcelona:

Kofin La Liga guda 10: 2004-05, 2005-06, 2008-09, 2009-10, 2010-11, 2012-13, 2014-15, 2015-16, 2017-18, 2018-19

Copa del Rey guda bakwai: 2008-09, 2011-12, 2014-15, 2015-16, 2016-17, 2017-18, 2020-21

Supercopa de Espana guda takwas: 2005, 2006, 2009, 2010, 2011, 2013, 2016, 2018

UEFA Champions League guda hudu: 2005-06, 2008-09, 2010-11, 2014-15

UEFA Super Cup guda biyu: 2009, 2011, 2015

FIFA Club World Cup guda uku: 2009, 2011, 2015

Kyautar da ya ci a Argentina tawagar matasa 'yan kasa da shekara U20:

FIFA U-20 World Cup: 2005

Kyautar da ya ci a Argentina tawagar matasa 'yan kasa da shekara U23:

Summer Olympics: 2008

Kyautukan da ya lashe a babbar tawagar Argentina:

Copa América: 2021; runner-up: 2007, 2015, 2016

FIFA World Cup runner-up: 2014

Kyautar da ya lashe ta kashin kansa:

Ballon d'Or/FIFA Ballon d'Or guda bakwai: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021

FIFA World Player of the Year: 2009

The Best FIFA Men's Player: 2019

Takalmin zinare a yawan cin kwallo a manyan gasar Turai guda shida: 2009-10, 2011-12, 2012-13, 2016-17, 2017-18, 2018-19

FIFA World Cup Golden Ball: 2014

La Liga Best Player: 2008-09, 2009-10, 2010-11, 2011-12, 2012-13, 2014-15

Argentine Footballer of the Year: 2005, 2007, 2008, 2009, 2010, 2011, 2012, 2013, 2015, 2016, 2017, 2019

Laureus World Sportsman of the Year: 2020

Ballon d'Or Dream Team: 2020