Hotunan yadda ake shirin zaɓen da za a kaɗa ƙuri'a da duwatsu a Gambia

Ga wasu zababbun hotuna na yadda ake kaɗa ƙuri'a da duwatsu a zaɓen da ake gudanarwa a ƙasar Gambiya.

Abokin aikinmu Zahradden Lawan ne ya aiko mana da su.

A ranar Asabar 4 ga watan Disamba ne al'ummar ƙasar Gambiya za su gudanar da zaɓuka.

Sai dai wani abin mamaki shi ne na yadda yawancin 'yan kasar na alfahari da salon yadda suke kaɗa ƙuri'a da ya bambanta da na sauran ƙasashe.

Da zarar sun isa rumfar zaɓe, bayan an kammala tantance su, za a nuna wa mai kaɗa ƙuri'a wani duro da aka yi wa fenti da alamar jam'iyyun siyasar ƙasar da ƴan takara.