Hotunan yadda ake shirin zaɓen da za a kaɗa ƙuri'a da duwatsu a Gambia

Ga wasu zababbun hotuna na yadda ake kaɗa ƙuri'a da duwatsu a zaɓen da ake gudanarwa a ƙasar Gambiya.

Abokin aikinmu Zahradden Lawan ne ya aiko mana da su.

Zaben Gambia 2021

A ranar Asabar 4 ga watan Disamba ne al'ummar ƙasar Gambiya za su gudanar da zaɓuka.

Sai dai wani abin mamaki shi ne na yadda yawancin 'yan kasar na alfahari da salon yadda suke kaɗa ƙuri'a da ya bambanta da na sauran ƙasashe.

Zaben Gambia 2021

Da zarar sun isa rumfar zaɓe, bayan an kammala tantance su, za a nuna wa mai kaɗa ƙuri'a wani duro da aka yi wa fenti da alamar jam'iyyun siyasar ƙasar da ƴan takara.

Zaben Gambia 2021
Bayanan hoto, Da zarar dutsen ya fada ciki zai yi ƙara, a nan ne jami'ai za su gane ko wani ya yi ƙoƙarin kada ƙuri'a sau biyu
Zaben Gambia 2021
Bayanan hoto, Wannan shi ne salon yadda ake ƙirga ƙuri'un duwatsun
Gambia
Bayanan hoto, Da zarar an rufe rumfunan zabe, za a ƙidaya duwatsun da ke cikin kowanne duro sannan a rubuta a jikin takardar da ke dauke da hoton dan takara da jam'iyyarsa
Zaben Gambia 2021
Bayanan hoto, Mutane sun shirya tsaf don jiran ranar zaben
Zaben Gambia 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A zaben da aka yi na baya, kamar na shekarar 2016, duro uku ne a kowacce runfar zabe dauke da hoton 'yan takara uku
Zaben Gambia 2021

Asalin hoton, Getty Images