Yara fiye da dubu 20 ne suka kamu da cutar HIV a Najeriya a bara- UNICEF

Asalin hoton, FLORENT VERGNES
Rahoton na asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce kananan yara daga kan jarirai zuwa 'yan shekara 9, fiye da dubu 20 ne suka kamu da ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki a Nijeriya a 2020.
Har wa yau, rahoton ya kara da cewa kimanin 30 cikin 100 na mace-mace masu alaƙa da cuta mai karya garkuwar jiki da suka faru a bara cikin Nijeriya, ƙananan yara ne.
Wannan batu dai ya zo wa 'yan Najeriya da dama da mamaki ganin yadda alkaluman suka harba sama.
To sai dai Abdulƙadir Ibrahim, babban jami'in gamayyar ƙungiyoyin masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki a Nijeriya wato NEPWHAN, ya ce alkaluman ba su zo musu da mamaki ba kasancewar yanzu haka a Najeriya da dama iyaye mata masu ciki ba sa iya samun damar yin gwajin kwayar cutar.
"Lokuta da dama za ka ga mace mai ciki ta zo asibiti amma sai ka ga babu kayan gwaji ko kuma idan ma da kayan sai a sanya kudi. Su kuma ka san matan karkara ba sa raina yawan kudi abin da zai sa su zuke su ki zuwa gwajin.
Hakan ne yake sa har mace ta samu juna biyu har ta sauka ta fara shayarwa ba za a gano tana dauke da kwayar cutar ba domin dakile shafa wa dan da ta haifa."
Abdulkadir ya kara da cewa "mu a yanzu muna da kididdigar a wannan watan kawai sama da yara dubu 150 wadanda aka dora a kan maganin kwayar cutar ta HIV."
Wadannan alkaluma dai na zuwa a dai-dai lokacin da duniya ke bikin ranar yaki da cutar mai karya garkuwar jiki ta HIV.
Yau ce dai ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin jan hankalin al`ummar duniya ga kokarin da ake yi wajen yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV ko SIDA.
A wannan shekarar, Majalisar Dinkin Duniyar ta ba da fifiko ne ga samar da daidaito a tsakanin masu fama da cutar fiye da mutum miliyon 37 ta fuskar samar da magani da kulawa.
Har wa yau, a irin wannan rana ana kuma mayar da hankali ga mutanen da suka harbu da cutar amma ba a gano su ba, domin cim ma kudurin dakile cutar nan da shekara ta 2030.
A Najeriya ma, mutum miliyon daya da dubu dari takwas ne suke fama da cutar, kuma mahukunta a kasar sun yi alwashin takaita yaduwar cutar nan da shekaru biyu masu zuwa wato zuwa 2023.











