Ranar yaki da cutar Sida: Karairayin da ake yadawa game da cutar HIV a shekarar 2021

Asalin hoton, Doreen Moraa Moracha
- Marubuci, Daga Rachel Schraer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and disinformation reporter
Lokaci na karshe da Paul Thornya ga iyayensa, sun jefar da kwanon da ya ci abinci a ciki saboda tsoron kar su dauki cutar. A lokacin da aka tabbatar yana dauke da cutar HIV a shekarar 1988, dole ta sanya ya daina aiki a matsayin jami'in lafiya.
"Na shafe shekaru 20 cikin fargaba," in ji shi.
A yanzu, da wuya Paul ya tuna da cutar a inda yake zaune a Birtaniya, abin da kawai yake tunawa shi ne lokacin shan magani a kowacce rana, da kuma ganin likita sau biyu a shekara.
Mutanen da ke dauke da cutar HIV, da kuma suke shan magani na gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata, su kuma more. Sannan an kawar da fargabar da ake yi a baya cewa idan kun ci abinci a kwano daya da mai cutar ana iya dauka. Sai dai har yanzu bayanan karya da ake yadawa kan cutar na ci gaba da yin tasiri.
'Akwai magani'
An haifi Doreen Moraa Moracha, 'yar kasar Kenya, da cutar HIV amma sai a shekarar 2005 ta san abin da ke damunta a lokacin tana da shekara 13.
Wani talla da ake yi a gidan talbijin din Tanzania ne ya kai ta ga wani mai maganin gargajiya, wanda ya ce zai iya warkar da Doreen da mahaifiyarta daga cutar HIV.
"Mun sha maganin gargajiyar da mai maganin yake sayarwa, mun koma gida da fatan mun warke daga cutar HIV", ta yi karin bayani. Sai ta daina shan maganin da likita ya ba ta na maganin, wanda ke rage kaifin cutar. Sannu a hankali sai ta fara tari da ciwon hakarkari, garkuwar jikinta ta yi rauni sosai.
Likitanta ya shaida mata cewa cutar ta karu a jininta, ta kuma kamu da wata cutar mai yaduwa da ka iya zama ajalinta.
Da kanta ta gane mai maganin gargajiyar dan damfara ne.
Sai dai Dakta Adeeba Kamarulzaman, kwararren likita kan cutuka masu yaduwa, kuma shugaban kungiyar masu dauke da cutar HIV, ya ce masu maganin gargajiya 'yan damfara sun dade suna cin karensu babu babbaka.
Kawo yanzu babu rigakafi ko maganin cutar HIV, duk da cewa an samu labaran mutanen da suka warke daga cutar da ya dan darsa kyakkyawan fata ga masu cutar. A cikin watan Nuwamba, wata mace 'yar Argentina ta zamo ta farko da ta kafa tarihin warkewa daga cutar HIV, bayan garkuwar jikinta ta yi yaki da ita.
'Za ka iya daukar cutar a kodayaushe'
Joyce Mensah 'yar Ghana ce da ta tsere zuwa Jamus domin gujewa tsangwamar da ake nuna mata, ta ce ta yi amanna rashin fahimtar cutar ya taka rawa wajen rasa aikinta, da gudunta da abokan hulda suka yi, hakan ya sa dole ta bar kasar ta.
Ta ce tsangwamar ta samo asali ne kan labaran karya da ake yadawa kan masu HIV, kullum a darare ake zaman cike da tsoro.
"Duk lokacin da wani ya adawa iyalai ko 'yan uwansa ya kamu da cutar HIV, abin da suka yi amanna da shi shi ne ana cike da hadarin kamu da cutar 100 bisa 100, da zarar an ce ka kamu shi kenan".
Da zarar mai cutar mai cutar ya fara shan magani na tsahon lokaci, da har ya sanya ba a ga wata kwayar cuta a jininsa ba, hakan ba tabbacin cewa ba zai iya shafawa wani cutar ba.

Asalin hoton, Joyce Mensah
Joyce uwace mai 'ya'ya hudu, ta kuma haife su a lokacin da take kan shan maganin cutar, babu daya daga cikinsu da ya kamu da cutar. Ana ba da kariya ga uwa mai dauke da juna biyu wajen haifar lafiyayyen jariri, ta hanyar magunguna kuma tun daga shekarar 2010 masu cutar ke haifar yara lafiyayyu.
Duk da haka, an koro 'yarta daga makaranta a Ghana, kan zargin ita ma tana dauke da cutar kuma za ta iya shafawa wasu.
Ian Green, babban jami'in kungiyar ba da agaji na Terrence Higgins Trust da ke Birtaniya, shi ma ya na dauke da cutar HIV, "Babban bayanin da ake yi ga masu dauke da cutar, da kuma ni ma na fuskanta, shi ne kallon kan ka amatsayin mai yada ta.
Shekara da shekaru, na shiga damuwa matsananciya, kan shafawa wani cutar. Sanin cewa ba zan iya shafawa wani cutar ba, ya sanya ni farin ciki".
'Cutar HIV ba matsala ba ce'
Yayin da fargabar mutuwa ta kau kan cutar HIV, mutane kuma suka fara sabawa da rayuwa da ita kamar babu komai, mai fafutuka na ganin an samu ci gaba.
"An samu gagarumin ci gaba a magance cutar HIV, sai dai tunanin da wasu ke yi na cewa an kawar da cutar, ta hanayr ayyukan da ake yi na daukar matakan kariya, hakan ba ya taimakawa, saboda rashin zuba kudade a fannin da za a ci gaba da magance matsalar baki daya," in ji Dakta Kamarulzaman.
HIV kawayar cuta ce da ke kassara garkuwar jikin dan adam, idan ba a yi maganinta ba sai ta rikide ta koma AIDS - wadda garkuwar jiki ba ta iya yakarta komai karfin magani.
A shekarar 2020, kusan mutum miliyan 38 ne ke dauke da cutar HIV a duniya, akalla 700,000 sun mutu sanadin rikidewarta zuwa AIDS, hakan na nufin ba a maganinta tun da fari ba.
Paul Thorn ya yi amanna matasan na kallon cutar a matsayin ta tsofaffi, wani batu da Ian Green na kungiyar agaji ta Terrence Higgins ke cewa "akwai kamfar bayanan wayar da kai kan cutar... Sun dauka cewa babu cutar HIV".
'Ba na cikin masu kamuwa da cutar HIV'
Kamar yadda matasa ke kallon cutar a matsayin ta tsofaffi yawanci ana kallon 'yan Luwadi ne kadai ke kamuw da ita.
A duniya baki daya, kusan rabin mai cutar HIV mata ne, kuma ita ce cutar da ke hallaka mata kamar wutar daji kamar yadda Christine Stegling ta kungiyar sa-kai dan wayar da kan jama'a kan cutar AIDS.
Sai dai kadan daga cikin matan da ta zanta da su, sun san hadarin da suke ciki na kamuwa da cutar.
"Ya na da muhimmancia samu kididdiga ta hanyar tattaunawa da matan da ke cikin shekarun kuruciya, wadanda za su iya daukar ciki, ayi musu bayani kan illar yin jima'i ba tare da kariya ba," in ji ta.
Ya yin da aka samu gagarumin sauyi a yaki da HIV, a bangare guda kuma ana ci gaba da yada labaran da ba su da tushe bare makama da ke jefa rayuwar masu cutar cikin hadarin ras aikin yi, ko samun maganin da ya dace ga wadanda ke dauke da cutar.










