World Aids Day: Ranar yaƙi da cutar HIV/AIDS ta duniya ta 2020

Yadda ake daukar jinin mutum domin gwajin cuta

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da aka ware kowacce ranar 1 ga watan Disamba domin tunawa da Ranar Cuta mai Karya Garkuwar Jiki ta Duniya, masana sun yi tsokaci a kan girman cutar da ma yadda mutane suka ɗauketa.

Mai Martaba Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sani Sami, wanda ke da wata ƙungiya mai suna Sami HIV/AIDS Trust da ke wayar da kai game da wannan cuta a jihar Kebbin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, jahilci shi ne babban abin da ke jawo musu cikas a yaƙin da ake da cutar HIV a Najeriya.

Ya ce: "Musamman a arewacin Najeriya idan dan abu ya sameka ka je asibiti an yi maka magani ka sake komawa ba sau ɗaya ba sai ace ai ciwon daji ke damun mutum".

Sannan kuma idan mutum ya kamu da cuta kamar ta HIV sai a ƙyamace shi har ma a daina zuwa kusa da shi, sannan kuma ace wai babu magani da dai sauransu, in ji mai martaba sarkin Zuru.

Alhaji Muhammad Sani Sami, ya ce akwai abubuwa da dama da ake faɗakar da mutane a kai ta yadda za su kare kansu daga kamuwa da wannan cuta.

Ya ce,"Kamar gidauniyata, mu kan je asibitoci ko makarantu da dai sauran muhimman wurare domin mu faɗakar da mutane a kan wannan cuta dama illolinta".

'Magidanta sun fi yaɗa HIV/AIDS'

Mai Martaba sarkin na Zuru, ya ce: "A gaskiya batun cewa akwai rahotannin da ke nuni da cewa magidanta sun fi kamuwa da cutar HIV, wannan gaskiya ne, domin al'ummarmu na da karan-bani sosai".

Sai dai babu wani bincike na fannin lafiya da ya tabbatar da hakan.

Ya ce,"Magidanta da yawa na kamuwa da wannan cuta har ma su je su yaɗawa iyalansu, muna da misalai da dama don haka idn muka samu irinsu sai muje gidajen mu yi musu nasiha gami da basu shawarwari a kan yadda zasu kula kansu".

Sarkin na Zuru ya ce, su ma a ɓangaren matasa, a kan basu shawara akan cewa kafin suyi aure to yakamata suje suyi gwaji don a tabbatar da lafiyar ma'auratan.

Haka kuma ya kamata daga matasan har magidantan su daina yawace-yawace na banza don kare kansu daga kamuwa da wannan cuta ta HIV, in ji Mai martaban.

Karin bayani

Masana kiwon lafiya dai na kara nanata cewa idan mutum ya kamu da cutar HIV, to ba shine karshen rayuwarsa ba, domin akwai maganin da ake sha, wanda idan har mutum ya kiyaye da ka'idar maganin to ba lallai ne idan aka ganshi ace ma yana da cutar ba.

Shirin haɗin gwiwa kan yaƙi da HIV da AIDS na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ƙiyasin mutum miliyan 38 ne ke fama da ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki a duniya, kuma sama da miliyan 35 ne suka mutu tun fara gano cutar a 1984.