Coronavirus: Ana amfani da magungunan HIV 'a kan masu cutar'

Yadda ake daukar samfurin jinin mutum ayi masa gwaji

Asalin hoton, Getty Images

Masu dauke da cutar HIV ko Sida sun yi korafi kan yadda gwamnatin kasar take amfani da magungunansu domin warkar da cutar korona.

Sun ce hakan ne ya sa magungunan nasu suka yanke, lamarin da ya jefa wasu masu dauke da cutar cikin mawuyacin hali.

Kaso 90 cikin 100 na maganin da masu cutar ta HIV ke amfani da shi na zuwa ne daga kasashen duniya a matsayin tallafi.

Wani jagora a kungiyar masu cutar a Najeriyar ya shaida wa BBC cewa, akwai magungunan da ya kamata ace gwamnatin kasar ta siya amma bata siya ba.

Ya ce "Wasu daga cikin magungunan da ake sha ma tun karshen shekarar 2019 suka kare, kuma rabon gwamnati da ta siya irinsa tun shekarar 2018".

Jagoran ya ce "Baya ga wadanda suka kare akwai kuma wadanda suka yi karanci koda yake mun samu labari cewa a kasuwannin duniya ma akwai karancinsa".

Ya ce akwai daya daga cikin magunguna da masu cutar ke sha da ake yi wa masu cutar korona amfani dashi, ba a Najeriya kadai ake amfani dashi ga masu korona ba, har ma a wasu kasashen duniya.

Jagoran ya ce "Na kira shugaban kwamitin shugaban kasa da ke yaki da cutar korona na shaida masa cewa an yi mana amfani da magani a kan masu cutar korona kuma gwamnati ta gaza siyo mana shi".

Ya ce " Ba zai yiwu gwamnati ta gaza siyo mana maganin dan kalilan da turawa suka kawo mana ba, sannan a dauki namun a rinka yi wa masu cutar korona magani ba".

Ya ce a dalilan rashin wasu magungunan ko kuma karancinsu, akwai wadanda ke da cutar HIV din da a yanzu ko mutuwa aka ce sun yi ba mamaki.

Jagoran ya ce, suna kira ga gwamnati da ta taimaka a samar musu da magungunansu saboda gudun fadawa mawuyacin hali.