Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Iran za ta sauka daga bakarta a yarjejeniyar makamashin nukiliya da Amurka?
Masana harkar siyasar duniya na yi wa tattaunawar da manyan kasashen duniya ke yi da Iran kan shirinta na mallakar makamashin nukiliya, kallon wani abun da ba zai dore ba.
A ranar Litinin ne dai manyan kasashen duniya suka fara gudanar da wata muhimmiyar tattaunawa da Iran, a birnin Vienna, da manufar farfado da tsohuwar yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran, watanni biyar bayan dakatar da ita.
Jami'ai na tattauna yiwuwar komawar Amurka cikin yarjejeniyar ta 2015, wadda ta iyakance harkokin nukiliyar Iran inda ita kuma Amurka za ta ɗage takunkuman da ta kakaba wa Iran.
Iran dai ta saɓa muhimman alƙawurra na yarjejeniyar tun bayan jenyewar Amurka a zamanin mulkin Donald Trump a 2018, inda ya sake ƙaƙabawa Iran takunkumai.
Yanzu haka shugaba Joe Biden na da niyyar ɗage su matuƙar Iran za ta koma kan iyakar da ta tsallaka. Sai dai Iran na cewa Amurka ce ya kamata ta fara ɗaukar mataki.
Iran ko Amurka - Wane ne zai sauka daga bakarsa?
Malam Muhammad Sidq Isa masanin harkokin siyasar gabas ta tsakiya ya ce a tunaninsa wannan sake zaman tattaunawa domin farfado da yarjejeniyar 2015 zai samu nakasu bisa la'akari da yadda kowanne daga cikin kasashen biyu ke ji da kansa.
"Ba na jin Iran za ta hakura ta yi duk abin da Amurka ke so kasancewar Iran ta san muhimmancin mallakar makamashin nukiliya a wannan zamani musamman a burinta na zama mai fada a ji a yankin Gabas ta Tsakiya.
To ita ma kuma Amurka da wuya ta sarayar da tata damar domin babu abin da ke tsone mata ido illa ta ga Iran ta mallaki makamashin."
To sai dai Qaddam Sidq Isa ya ce "Amurka ce ya kamata ta fara kwaye wa Iran jerin takunkumai kafin daga bisani kuma ita Iran ta rage yawan matakin shirin makamashin na nukiliya."
Amma jakadun kasashe sun nuna kwarin gwiwa da kyakkyawan fata na cimma matsaya duk da dan nakasun da aka samu kan matsayar Iran da Amurka.
Wakilan Kungiyar tarayyar turai da na Rasha da Iran duka sun bayyana kyakkyawan fata a karshen taron na sa'a biyu.
Shi ma Shugaban Faransa, Emmanuel Macron yayin wata tattaunawa da Shugaban Iran Ebraihim Raisi ta waya, ya bukaci Iran din da ta bude zuciyarta yayin zaman.