ASUU: Abu hudu da majalisar wakilai ta ce ta cimma da ƙungiyar malaman jami'a ta Najeriya

Asalin hoton, @HouseNGR
Majalisar wakilan Najeriya ta ce ta yi tattaunawa ta fahimta da shugabannin kungiyar malaman jami`o`i game da barazanar shiga yajin aikin da kungiyar ke yi.
Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci zaman, kuma ministocin kudi da na ilimi duka sun halartarci zaman.
Shugaban kwamitin majalisar kan manyan makarantu Hon Aminu Sulaiman Goro, ya fada wa BBC cewa a yanzu an samu fahimtar juna a tsakanin duka bangarorin, kuma an daidaita da malaman jami`ar ta yadda ba sauran fargaba game da barazanar yajin aikin da ƙungiyar ke yi.
Honarabul Suleiman Goro ya bayyana abubuwa hudu da aka cimma kan bukatun ASUU:
Farfado da jami'o'i
Abu na farko da ɓangarorin suka cimma shi ne batun biyan kudin farfado da jami'o'in ƙasar da ASUU ta kira 'revatalization fund'.
Dama ƙungiyar malaman makarantar ta dade tana kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wannan kuɗi da ya haura sama da naira tiriliyan daya, don farfaɗo da jami'o'in kasar da suka lalace ko kuma suke buƙatar gyara.
Gwamnatin Najeriya ta ce naira biliyan 230 ne za ta iya bai wa ASUU a matsayin kudin, don yin kwaskwarima ga jami'o'in.
Kuma kafin a tafi ko'ina ɓangaren gwamnatin ya ce zai ba da kason farko na naira biliyan 30 a yan kwanaki masu zuwa.
Biyan kudin alawus
Batun ƙin biyan alawus-alawus na daga cikin abubuwan da aka daɗe ana kai ruwa-rana da kuma malaman jami'o'i a Najeriya ke ƙorafi akai.
Kuma a lokuta da dama batun na daga cikin abubuwan da ke malaman jami''o'in shiga yajin aiki.
Amma majalisar ta ce zaman da ta shiga tsakani, gwamnati ta aminta cewa a cikin mako mai zuwa za ta biya naira biliyan 22, da za a raba tsakanin malaman jami'o'in da kuma ma'aikatan lafiya.
Tsarin albashin IPPS
Batun tsarin samar da bayanan ma'aikata game da abin da ya shafi biyansu albashi na IPPS, na daga cikin abubuwan da suka kara dagula al'amurra tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU.
Tun bayan ɓullo da tsarin na IPPS da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi malaman jami'o'in ke adawa da shi.
Kuma ga alama ko yanzu suna nan kan bakarsu, duk da sun gabatar da wani tsari na daban da suke bukatar a dora su akai.
Amma a nan bangaren gwamnatin ya ce zai aminta da hakan, matsawar hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta kasar wato NITDA ta tantace tare da amincewa da tsarin.
Sauran korafe-korafe
A karshe kuma duka ɓangarorin sun aminta majalisar wakilan ta ci gaba da shiga tsakani tare da duba sauran korafe-korafen da ASUU ke da su.
A cewar Hon Aminu Sulaiman Goro "an kafa kwamiti dole a zauna a duba dukkan waɗannan yarjejeniyoyi, a san wane ne zai yiyu da wanda ba zai yiyu ba, don a ga cewa an daina rufe jami'o'i da sunan yajin aiki."
Sai dai a karshe wakilan ASUU sun ce za su koma su sanar da mambobinsu matsayar da aka cimma.
Kazalika sun bukaci a ba su yarajejeniyar da aka cimma a rubuce don kafa hujja da kuma daukar mataki na gaba.

Me ASUU ta ce game da yajin aiki?

Asalin hoton, @HouseNGR
Zuwa yanzu ƙungiyar ASUU ta ce ba ta ɗauki matakin shiga yajin aiki ba bayan barazanar wa'adin mako uku da ta ba gwamnati.
Shugaban ƙungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya shaida wa sashen BBC na Pidgin cewa bayan wa'adin makwanni uku da ƙungiyar ta ba gwamnati, ƙungiyar za ta sake zama domin yanke shawara kan matakin da za ta ɗauka na gaba.











