Dokar karatun ba-daya da aka amince a 1999, ta ce dole gwamnati ta bayar da ilimin firamare na shekaru shida kyauta. Sannan dalibai za su shiga matakin farko na karatun sakandare ba tare da an biya kudi a jiha ba.
Babu inda aka ambaci daidaito wajen ilmantar da yara maza da mata, amma a Najeriya yara maza ne suka fi zuwa makaranta fiye da mata - Duk a cikin mata tara a makaranta akwai maza guda 10.
An fi ba da muhimmanci kan kara yawan dalibai mata a makarantu
Hukumar kula da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya Unesco ta kayyade daidaito tsakanin maza da mata inda ta ce idan aka samu maza 100 a makaranta ya kamata a ce an dauki mata 98 zuwa 102.
A cewar wani bincike kan ilimi a 2016, kasa da jiha daya cikin uku ake samun daidaiton jinsi a makarantun firamare. A matakin farko na sakandare kuma jihohi tara ne, jihohi uku kuma a matakin karshe na sakandare
Jihar Ekiti ce kan gaba wajen samun daidaito tsakanin maza da mata a duk matakin na ilimi a jihar.
Jihar Katsina ce ta karshe da aka fi samun rashin daidaito a dukkanin matakan ilimi bisa ga yawan dalibai a makarantu. An dauki sama da yara maza 170,000 fiye da mata a makarantun firamare; sama da maza 43,000 fiye mata a matakin farko na sakandare da kuma maza sama da 44,500 fiye da mata a matakin karshe na sakandare.
Jihar Zamfara ce mafi muni ta la'akari da yawan daliban da aka dauka a makarantu a dukkanin matakai na ilimi inda adadin maza ya lulluka na dalibai mata.
Ingancin ilimin da wadannan daliban ke samu shi ma wani batun diba wa ne. Sakamakon wani binciken ilimi na 2015 (NEDS), ya nuna cewa kashi 44 na daliban da ke makarantun firamare na gwamnati sun iya karatu, amma a makarantu masu zaman kansu kashi 74 ne suka iya karatu. A matakin sakandare kuma a makarantun gwamnati kashi 91 ne yayin da masu zaman kansu kashi 96.
Shugaba Buhari ya yi alkawalin ware wa ilimi kashi 15 a kasafin kudi, amma ayyukansa tun hawansa ya nuna akwai bukatar mayar da hankali sosai domin cimma wannan burin
A 2016, kashi takwas gwamnatinsa ta ware wa ilimi a kasafin kudi, a 2017 adadin ya ragu zuwa kashi 7.4. A 2018 kuma an sake ware wa ilimi kashi bakwai daga kasafin kudin wato Naira biliyan 650.
Domin cika alkawalin da ya dauka na ware wa ilimi kashi 15 a kasafin kudi, shugaban dole sai ya lunka kudaden da yake ware wa ilimi wato naira tiliyan 1.3, ko ya rage kudaden da aka ware wa wani bangare.