Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
ASUU: Yaushe kungiyar malaman jami'a za ta daina yajin aiki?
Tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar malaman jami'a ta ci tura lamarin da ya jefa dubban daliban kasar cikin mawuyacin hali.
Hakan ya sa dalibai kamarsu Olamide Tejuoso wadda ke fatan soma shekarar 2019 za su ci gaba da zaman gida.
Ta so kammala karatun digirinta domin ta soma aiki da wani kamfani a matsayin mai samun horon aiki. Matakin farko da take son dauka domin zama marubuciya bayan ta kammala digiri a jami'ar Ibadan.
Sai dai maimakon hakan, wannan daliba da take karatu a fannin aikin jarida, ta fada cikin matukar damuwa saboda yajin aikin da malaman jami'a ke yi.
Malaman sun zargi gwamnati da kin yin biyayya ga yarjeniyoyin da suka kulla a baya game da inganta tsarin karatun gaba da sakandare.
Sun daka yajin aikin ne saboda ba a bai wa makarantun kudaden da suka kamata da kuma rashin gine-gine da ma yunkurin kara kudin makaranta.
Ranar Litinin kungiyar malaman jami'a da ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige sun yi taro inda suka ce sun cimma matsaya. Gwamnati na shirin bai wa jami'o'in 15.4bn naira.