ISWAP: Yadda mayakan ke tilasta wa ƙauyuka biyan haraji a matsayin zakkar amfanin gona a Borno

Mazauna wasu kauyukan Borno na kuka da yanayin da suka tsinci kansu na tilasta biyan haraji ga 'yan bindiga a matsayin zakkar amfanin gona.
Mazauna kauyukan yankin Damboa sun ce 'yan bindiga na amfani da karfi wajen karɓe musu amfanin gona da dabobbi, kuma su na yi musu biyayya domin tsira daga barazanarsu.
Wannan batu na sake fitowa fili a daidai lokacin da aka ci gaba da raɗe-raɗin cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP na karbar haraji daga hannun manoma da makiyaya a Borno.
Mayaƙan dai kan bai wa manoma damar ci gaba da aikin gona, bisa sharaɗin za su biya haraji ko zakka bayan sun yi girbi.
Yankin na Damboa mai maƙwabtaka da garin Chibok, na cikin yankunan da suke fama da hare-haren Boko Haram.
Yadda suke karbar harajin
Ɗan majalisar jihar Borno mai wakiltar Damboa Hon Malami Wakil Korede ya shaida wa BBC cewa tsakanin Damboa da Biu akwai wasu kauyuka biyu da 'yan bindiga ke sheke ayarsu, saboda babu mutane sosai a yankin.
Ya ce har shinge suka sa, kuma ba wai manoma kadai da makiyaya suke bi ba, har motoci da ke ratsa yankin ana karbar kuɗaɗe a hannunsu.
Hon Malami ya ce: "Suna saukar da mutane su bincikesu, kuma manyan mutane da ma'aikatan gwamnati sun ƙaurace wa yankin saboda rashin tsaronsa.
"Ba wai kuɗi kawai suke karba ba, abubuwan da suke karba sun hada da amfanin gona da shanu kuma dole ka bada abin da suka yanke."
Ɗan majalisar ya ce duk wanda ya ƙi musu biyayya, suna iya hallaka shi, sannan babu wani abin da hukumomi ke yi a yanzu saboda abubuwan sun yi yawa, amma dai ana kan kokari a wasu yankunan.
Ya ce akwai kuma karancin labari ko musayar bayanai da za su iya taimaka wa wajen fatattakar 'yan bindigar.
'Cin-karensu ba babaka'
Wannan yanayi da mazauna kauyukan Damboa ke ciki na sake bankado irin matsalolin tsaro da wasu kauyukan Borno ke ciki har yanzu, inda ko a yammacin Litinin an samu rahotanni da ke cewa an ƙona gidaje a wani hari da mayaƙan Boko Haram reshen ISWAP a yankin Askira Uba suka kai.
Harin na zuwa ne kwana biyu bayan mummunan harin da ya yi sanadin kashe sojojin Najeriya ciki har da wani mai muƙamin janar.
Ita ma rundunar sojin ƙasar a wata sanarwa da ta fitar a yammacin Litinin, ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram 50 a harin ramuwar gayya da suka ƙaddamar bayan yunƙurin kutsawa cikin garin Askira na ranar Asabar, da bai yi nasara ba.
Wata jaridar intanet a ƙasar ta ce sojoji sun sanya dokar hana fita a garin na Askira da kewaye.
Jaridar PRNijeriya ta ce mayaƙan ISWAP sun ƙaddamar da sabon harin ne a kan ƙauyen Dille, amma cikin nasara haɗin gwiwar dakarun sojin sama da na ƙasa na Najeriya suka wargaza shi.
Jaridar ta ambato wata majiyar tsaro na cewa sojojin sun samu bayanan sirri cewa mayaƙan ISWAP sun durfafi gadar ƙauyukan Wamdeo ta Gabas da kuma Roumirgou a yankin Askira Uba, lamarin da ya sa suka zauna cikin shiri.
Sai dai, jaridar Daily Trust ta ce mayaƙan na Boko Haram sun ƙona gidaje a ƙauyen na Dille, bayan sun far wa yankin da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
Ta ambato wata majiya na cewa maharan sun wawashe shaguna da yawa, inda suka yi awon gaba da kayan abinci kafin su cinna wuta a kan gidaje.
Zuwa maraicen Litinin babu masaniya takamaimai ko mutum nawa harin ya shafa.
Mutuwar sojoji
Harin na zuwa ne daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta sake fitar da ƙarin bayani kan arangamar dakarunta wadanda ta ce sun bi sawun mayaƙan ISWAP da suka kai mummunan harin ranar Asabar wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin ƙasar ciki har da Janar Dzarma Zirkusu.
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP 50 tare da lalata kayan yaƙinsu da dama.
Ta ce yayin arangamar an kuma kakkaɓe manyan kwamandojin ISWAP tare da lalata motarsu mai sulke da sauran motocin da ake girkawa manyan bindigogi guda 11 a ƙauyen Leho, baya ga bindigogi iri daban-daban da ta ce dakarun sojin Najeriya sun ƙwace.











