Malala Yousafzai ta zama amarya

Malala da angonta Asser

Asalin hoton, AFP

Fitacciyar yarinyar nan mai fafutikar kare hakkin mata, Malala Yousafzai, wadda kuma ta samu kyautar Nobel ta zaman lafiya ta yi aure.

Matashiyar mai shekara 24, ta sanar da auren nata a shafinta na Tiwita, inda ta ce ita da iyalanta sun gudanar da dan karamin bikin auren a gidansu da ke birnin Birmingham a Birtaniya.

Ta shaida wa kusan masu bibiyarta a shafin kusan miliyan biyu cewa ''wannan rana ce mai cike da farin ciki a rayuwata,'' inda ta bayyana sunan mijin nata Asser.

Malala ta yi fice a duniya tana da shekara 15, lokacin da mayakan Taliban suka harbe ta a ka, kan hanyarta zuwa makaranta, saboda fafutukar da take yi kan ilimin 'ya'ya mata a kasarta ta haihuwa Pakistan.

Malala tare da iyayenta da ango Asser

Asalin hoton, MALIN FEZEHAI

Mutane sun yi ta tururuwa shafin Malala domin taya ta murnar auren da ta yi

Asalin hoton, MALIN FEZEHAI