David Fuller: An fara bincike kan mutumin da ya yi lalata da gawa 100

Asalin hoton, Kent Police
Sakataren lafiya na Birtaniya ya ƙaddamar da kwamitin bincike mai zaman kansa bayan da wani ma'aikacin wutar lantarki a asibiti ya shiga dakin ajiye gawa domin ya yi lalata da su.
David Fuller, mai shekara 67, ya dauki hoton kansa yana lalata da akalla gawarwaki 100 a wasu wuraren ajiye gawawwaki biyu na asibitin Kent sama da shekaru 12 da suka gabata.
Hakan ya biyo bayan Fuller wanda ya fito daga Heathfield da ke Gabashin Sussex, ya amince da kashe Wendy Knell da Caroline Pierce a 1987.
Sajid Javid ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa binciken zai duba laifukan da "illar da hakan ya janyowa kasa".
Ya ce: "Zai taimaka mana mu fahimci yadda wadannan laifuka suka faru ba tare da sanin mahukuntan asibitin ba, tare kuma da tantance wuraren da ya kamata a ce an dauki mataki cikin gaggawa, sannan kuma zai yi nazari a kan wasu manyan batutuwan da suka shafi tsarin kiwon lafiyar kasar ciki har da hukumar lafiya ta NHS."
An raba binciken gida biyu, za a wallafa rahoton wucin gadi a farkon shekara mai zuwa yayin da rahoto na ƙarshe wanda zai dubi girman matsalar da kuma darussa da NHS za ta koya.
Wani ƙwararren likita a kwalejin horar da likitoci ta Royal, Sir Jonathan Michael ne zai jagoranci binciken.
Zai maye gurbin wani bincike mai zaman kansa, kamar yadda Mista Javid ya fadawa majalisar dokoki.
Ya kuma ce za a sake duba hukuncin da ake da su kan "munanan" laifukan da suka shafi lalata bayan shari'ar don tabbatar da cewa "sun dace".
''Ina so na nemi afuwar abokai da iyalan duk wadanda aka ci zarafinsu ta hanyar lalata karkashin kulawar NHS," Mista Javid ya kara da cewa.
"Babu wani abu da za mu iya cewa da zai gyara ɓarnar da aka yi, amma dole ne mu dauki mataki domin ganin cewa babu wani abu makamancin haka da zai sake faruwa."

Asalin hoton, Kent Police
Fuller ya ajiye miliyoyin hotuna da bidiyo na laifukan da ya aikata a dakunan ajiye gawarwaki a faifai.
Ya ɗauki hotunan ne tsakanin 2008 da Nuwamba 2020, kuma ya sanya sunayen wadanda ya yi lalata da su a faifain.
Fuller ya yi aiki a asibitoci daban-daban tun 1989 kuma ya yi aiki a asibitin Kent da Sussex har sai da aka rufe a watan Satumba 2011.
An mayar da shi Asibitin Tunbridge Wells da ke Pembury, inda ya ci gaba da aikata laifuka har zuwa lokacin da aka kama shi a shekarar 2020.
Masu binciken sun ce Fuller ya riƙa aiki da daddare kuma yana shiga dakin ajiyar gawa lokacin da sauran ma'aikatan suka tafi.

Sharhin wakiliyar lafiya ta BBC, Catherine Burns
Binciken farko na kwamitin zai fi mayar da hankali ne kan binciken da asibitin Maidstone da Tunbridge Wells ya yi.
Zai bayar da rahoto a cikin sabuwar shekara kuma ya yi ƙoƙarin gano duk wani aiki da yake buƙatar ɗauka.
Kashi na biyu zai dauki tsawon lokaci, saboda yana da fadi sosai. Zai kuma dubi darussan da ya kamata hukumar lafiya ta NHS ta koya, da kuma shugabannin gidajen ajiye gawarwaki na ƙananan hukumomi da kuma masu zaman kansu.
Sajid Javid ya kuma yi magana a kan iyalan wadanda abin ya shafa. Kamar yadda ya ce, "Mutanen da suka riga sun sami irin wannan asara kuma yanzu suna fuskantar takaici da fushi mara misaltuwa".
Wasu daga cikin iyalan sun riga sun dauki lauya kuma suna tunanin daukar matakin shari'a a kan asibitin.
An samu David Fuller da laifi, amma 'yan sanda ba su kamala bincike ba. Jami'ai na ci gaba da nazarin hotunansa da bidiyonsa.
Ana sa ran ci gaba da yin hakan na tsawon wata guda ko makamancin haka. Sun yi nuni da cewa ba za a taba gano wasu da abin ya shafa ba.

Sanarwar Mista Javid na zuwa ne bayan da 'yan majalisar dokokin da ke wakiltar mazabun Kent da Sussex su ka aike wa sakataren kiwon lafiya da wasikar hadin gwiwa in da suka nemi a kaa komitin bincike a kan gawarwakin da aka yi lalata da su a dakin ajiye gawawwaki.
A Majalisar dokoki dan majalisa mai wakiltar Tunbridge Wells Greg Clark ya nemi Mista Javid ya tabattar cewa kwamitin ya ba iyalan wadanda al'amarin ya shafa damar gabtar da shaida a kan yadda laifukan suka shafi rayuwarsu.
Ya kuma tambayi Mista Javid ko zai ba da shawarwari ga hukumar ta NHS, ya kuma kara da cewa: "Shin zai buga ƙimanta hadarin da ke tattare da sauran sassan da ake ajiye gawarwakin mutane?"
Mista Javid ya tabbatar da cewa binciken zai yi dukkan abubuwa uku.
A baya 'yan sandan Kent sun ce an yi kira 403 a wayar 'yan sanda, wanda aka kafa domin mutanen da ke da bayanai game da binciken.












