Mali: ECOWAS ta sanya wa mambobin gwamnatin rikon-kwarya takunkumi

Kanar Assimi Goïta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jagoran juyin mulkin Mali Kanar Assimi Goïta wanda ya nada kansa shugaban rikon-kwarya

Shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, sun sanya takunkumi a kan mambobin gwamnatin rikon kwarya ta Mali tare da iyalansu.

Takunkumin ya kama ne daga hana tafiye-tafiye da kuma na dakatar da kadarori.

Matakin ya biyo bayan gazawarsu ta bin jadawalin da aka fitar na mayar da kasar ga tsarin mulkin farar hula zuwa watan Fabrairu na shekara mai zuwa.

A yayin wani taro na musammana da suka yi a birnin Accra, na Ghana, a jiya Lahadi, shugabannin kungiyar ta Yammacin Afirka, sun yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen aiwatar da takunkumin.

A wata sanarwa da shugabannin yankin na Afirka ta yamma suka fitar sun nuna cewa, za su duba yuwuwar sanya karin takunkumi a kan kasar ta Mali, idan suka sake haduwa a watan gobe, wato Disamba.

Sun tabbatar da cewa hukumomin kasar sun sheda musu cewa ba za su iya cimma wa'adin da suka diba ba, na rikon kwarya tare da gudanar da zabe a watan Fabrairu na shekara mai zuwa.

Haka kuma shugabannin na ECOWAS ko CEDEAO sun yi Allah-wadarai da korar wakilin dindin din na kungiyar a Mali tare da yin kira ga hukumomin kasar da su bayar da haddin kai domin shawo kan matsalar siyasar kasar.

Kungiyar ta kasashen Yammacin Afirka ta dage takunkumin da ta sanya wa Mali bayan da soji suka yi juyin Mulki a shekarar da ta wuce, sakamakon yarjejeniyar da aka cimma da sojin ta tabbatar da mayar da mulki hannun farar hula a cikin wata 18.

A game da Guinea, kuwa kungiyar ta ECOWAS ta sake yin kira da a saki hambararren shugaban kasa Alpha Conde, tare da neman gwamnatin sojin kasar da ta mika jadawalin mayar da kasar mulkin farar hula.

Alpha Condé a 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hambararren shugaban Guinea Alpha Condé a 2020

Dukkanin kasashen biyu Mali da Guinea an kore su daga cikin kungiyar ta kasashen ammacin Afirka saboda juyin mulkin da soji suka yi kwana nan.