Bikin Diwali: Wasan wuta a bikin ya gurɓata iskar birnin Delhi na Indiya

Asalin hoton, ANI
Hazo ya lulluɓe Delhi babban birnin Indiya bayan bukukuwan Diwali da aka gudanar a ƙasar.
Duk da haramcin amfani da kayan wasa masu fitar da hayaki, mutane a faɗin kasar sun yi ta amfani da su har cikin daren Alhamis kuma hakan ya ƙara gurɓata yanayin birnin.
Gurɓataccen hayaƙi wanda motoci da masana'antu ke fitarwa tare da ƙura da sauyin yanayi sun sa Delhi ya zama birni mafi gurɓacewar yanayi a duniya.
Iskar birnin ta zama gurɓatacciya a lokacin hunturu lokacin da manoma a jihohi maƙwabta ke ƙona ciyawa.
Tartsatsin wuta da ake wasa da shi a lokacin bikin Diwali, wanda ake yi a lokaci guda da manoman ke ƙona yayi, na ƙara gurɓata muhali.
Gwmmnatin kasar ta hana sayar da kayan tartsatsin wuta da kuma wasa da su a bana domin rage gurbata muhalli. Sai dai alamu sun nuna cewa wannan bai hana mazauna birnin wasa da wutar ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hayaki ya turnike birnin da safiyar Juma'a kuma mutane sun koka da ciwon makogwaro kuma idanuwansu na ruwa.
Rashin kyawun yanayi na cikin abubuwan da suka janyo haɗarin mota shida da aka yi a wata babbar hanya, wanda ya jikkata mutane da dama ciki har da yara, kamar yadda NDTV ta ruwaito.
An yada hotona da bidiyon hatsarin a shafukan sada zumunta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wasu sun yi korafi kan yadda ake saurin hasashen samun matsalar gurbata muhali a kowace shekara a lokacin Diwali.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

Sai dai kuma batun ya rikide zuwa siyasa inda wasu ke kallon hakan a matsayin wani yunkurin shafa wa bukukuwan Hindu kashin kaji. Suna jayayya cewa wasan wuta na Diwali wani ɓangare ne na bikin kuma ba su da alhakin gurbata muhali saboda Delhi ta saba fuskantar matsalar iskar da ke gurbata muhali a duk shekara.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Mutane da dama sun rika wallafa hotunan kansu da suka dauka a shafin Twitter suna cewa ta wannan hanyar ce suke son su yi bikin Diwali.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4

Amma wasu suna jayayya cewa yawan wasan wuta yana ƙara tsananta samun iskar da ke gurɓata muhali - kuma bayan tartsatsin wutar ana bikin kunna fitilu tare da adu'a ga gunkin Lakshmi don samun wadata.
Jami'ai sun ce yanayin zai ɗan inganta ne kawai nan da yammacin Lahadi.
Hukumar sa ido kan ingancin iska ta kasar ta yi kiyasin cewa konewar ciyayi ne yake samar da kashi 35 cikin 100 na iskar da ke gurbata muhali a Delhi ranar Juma'a, kuma da alama zai kau a karshen mako.
Indiya ce ke da gurbacewar iska mafi muni a duniya. Tana da garuruwa 22 daga cikin 30 da suka fi gurbacewar yanayi a duniya.
Iskar mai guba ta Indiya na kashe mutane sama da miliyan ɗaya a kowace shekara, a cewar masana.
Binciken baya-baya nan ya nuna cewa mutum 480 a arewaciin Indiya na fuskantar ''matsanancin hayakin da ke gurbata muhali a duniya''.