Diwali 2021: Indiyawa na bikin fitila na Diwali

Asalin hoton, Getty Images
Indiyawa na kunna wuta su ajiye cikin launuka, yayin da miliyoyin mutane mabiya addinin Hindu ke bikin Diwali. Amma bikin na bana yazo lokacin da ake da matukar damuwa kan annobar korona da kuma gurbatar muhalli.
Lokacin bikin addini ne, a yi addu'a da kuma kunna wuta.
Bikin Diwali na daya daga cikin bukukuwa mafiya mahimmanci a Indiya.
An fi sanin wannan bikin da bikin fitila yayin da mutane ke ajiye wani dan kwano dauke da mai da wuta a ciki da kuma kyandir domin nuna farin ciki kan nasarar da haske ya samu kan duhu da nasarar da mutanen kirki suka samu kan azzalimai.
Bikin na bana na nuni da yadda korona ke ci gaba da janyo asarar rayukan mutane.
Duk da cewa adadin mutanen dake mutuwa saboda cutar na raguwa idan aka kwatanta da watannin baya, Indiya na daya daga cikin kasashen da wannan annoba ta yi wa illa, inda a hukumance mutum miliyan 35 suka kamu da cutar kuma sama da mutum 45,000 suka mutu.
A wajen wasu da dama, Diwali wata alama ce ta shiga sabuwar shekara. Wani lokaci ne da ake farin ciki da murna - ake yin shagali, lokaci ne da mutane ke haduwa da abokai da iyalansu a kuma rika bai wa juna kyautuka.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Ranar da ake yin bikin na sauyawa ko wacce shekara kuma yadda wata ke sauyawa ne ke nufin ranar da za a yi bikin.
Sai dai an fi yin bikin tsakanin watannin Oktoba da Nuwamba.
A wannan shekarar an fara bikin Diwali ne ranar Alhamis.
A shekarar da ta gabata an dakatar da mafi yawan abubuwan da aka saba yi a bikin saboda korona.
Gwamnatin kasar ta roki mutane da su nisanci taruwa wuri guda kowa ya tsaya a gida ya yi bikinsa.
Kuma da yawa sun bi wannan doka, yayin da majami'u suka rika gudanar da ibadunsu a intanet tare da neman mabiya da su rika halarta ta kafar.
Amma a Delhi babban birnin kasar, an rika samun taron mutane a kasuwa gabanin babban bikin.
Hukumomi sun ce hakan zai iya jefa mutane cikin hadarin da zai janyo tabarbarewar tsarin kiwon lafiya a kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, SANJAY KANOJIA
Ba matsalar annobar ba ce kawai, yadda ake harba abubuwan fashewa sama na janyo gurbatar muhalli a kowacce shekara.
Wannan kuma ya fi muni a Delhi, inda hayaki yake baibaye samaniyar birnin.
Iskar garin ta gurbata a watan Nuwamba da Disamba yayin da su ma manoma a jihohin Punjab da Haryana ke kona sauran kayan amfanin gona domin gyara filin nomansu.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka











