Zaben Anambra: Buhari ya gaza idan ya kasa gudanar da zaɓen Jihar - Masani

Yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar Anambra da ke kudancin Najeriya wanda ke tattare da tarin ƙalubale, masana sun yi gargaɗin cewa dole ne gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi dukkan mai yiwuwa don gudanar da zaɓen.

Dakta Abubakar Kari, wani masanin siyasa a Jami'ar Abuja babban birnin Najeriya, ya ce gwamnati za ta ji kunya idan har ta kasa gudanar da zaben a lokacin da aka tsara.

A cewarsa, ''Wannan zaɓe na musamman ne, kana ma iya cewa shi ne zai iya kasancea ma zakaran gwajin dafi da zai nuna ko gwamnatin Najeriya na da karfin ikon gudanar da zaɓen a dukkan sassan Najeriya ba ma wai jihar Anambra kawai ba''

Ya ƙara da cewa ''Tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa za a sauya gwamnati duk bayan shekara hudu, don haka za mu ga ko ita gwamnatin Najeriya za ta buwayi wannan ƙungiya ta yi abin da take so, ko wasu tsurarun mutane za su iya yin abin da suke su''.

Masanin ya ce idan har kungiyar yan awaren ta IPOB ta yi nasarar hana gudanar da zaɓen kamar yadda ta lashi takobin yi ''To kaga kenan gwamnati ta gaza kenan, ta nuna cewa da gaske wasu ƴan tsiraru sun fi ƙarfinta, kuma hakan na nufin cewa ba ma yanzu ba ko nan gaba wasu za su iya hana ta yin wani abu da take son ta aiwatar''

Ita dai gwamnatin kasar Amurka ta bayyana fatan ganin an gudanar zaben gwamna a jihar ta Anambra ta yankin kudu maso gabashin Najeriya, cikin lumana da inganci.

A nata ɓangaren ita ma gwamnatin jihar ta dauki matakin bayar da hutu ga ma'aikata, tare da bayar da sanarwar rufe hanyoyin shiga jihar na dan wani lokaci, don ganin an gudanar da zaben yadda ya kamata.

Tun kafin karatowar zaben ne ƙungiyar ƴan awaren ta Biafra ta tsananta kai wa ofisoshin hukumar zaɓen Najeriya INEC da ke jihar hare-hare, da zummar hana gudaanr da zaɓen.

A halin da ake ciki an jibge dubban jami'an tsaro, kama daga na sojoji da yan sanda, da sauran takwarorinsu, don ganin an gudanar da zaɓen lami lafiya ba tare da wani tarnaƙi ba.