Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da aikin tituna a arewa maso gabas bayan rahoton BBC
Latsa hoton sama ku saurari hira da Babangida Hussaini, sakataren ma'aikatar ayyuka a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sake ware kuɗi domin ci gaba da ayyukan manyan hanyoyi uku bayan rahoton da BBC Hausa ta yi kan tsananin lalacewarsu a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Titunan sun haɗa da hanyar da ta tashi daga garin Cham na Jihar Gombe zuwa Numan na Jihar Adamawa da titin Gembu da ke haurawa tsaunin Mambila da kuma hanyar Gombe zuwa Biu.
Da ma dai gwamnatin ta bayar da aikin wasu daga cikin hanyoyin amma an shafe tsawon lokaci ba tare da gudanar da aikin ba.
BBC Hausa ta yi rahotanni kan tsananin lalacewar hanyoyin Gombe zuwa Numan da Numan zuwa Jalingo da kuma hanyar Gembu ne cikin wasu jerin rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba a watannin nan.

Babban sakataren ma'aikatar ayyuka da gidaje ta Najeriya, Babangida Hussaini, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin tarayya ta ware duka kudaden da ake bukata domin aikin hanyoyin da kuma karin wasu a fadin kasar.

Asalin hoton, BBC
Babangida ya ce kamfanin mai na NNPC ne zai samar da kuɗaɗen daga cikin harajin da ya kamata ya biya Najeriya.
Babban sakataren ya ce an ware wa titin Gembu, mai tsawon kilomita 110, naira biliyan 20 sannan kuma aikin zai ci gaba nan take.
Ya kara da cewa za'a tabbatar da 'yan kwangila sun yi aikin ba tare da inda-inda ba kasancewar ma'aikatar za ta dinga sanya ido kan yadda aikin ke gudana.
Kazalika, rahoton BBC kan aikin tashar lantarki ta Mambila ya jawo muhawara tsakanin 'yan ƙasa bayan shekara biyar gwamnatin Buhari na maganar aikin.
Rahoton ya gano cewa ko filin da za a yi aikin ba a gyara ba, wanda ke Jihar Taraba.
Titin Gombe zuwa Adamawa
A ranar 22 ga watan Oktoba ne BBC ta yaɗa rahoton mai taken "yadda gyaran babban titin Gombe zuwa Adamawa ke tafiyar hawainiya".
Matafiya da ke bin manyan titunan da suka hade jihohin Gombe da Adamawa da kuma Taraba sun sha kokawa kan tsananin lalacewar hanyoyi.
Lalacewar titunan dai tafi kamari ne daga garin Billiri zuwa Numan da kuma Numan zuwa Jalingo.
Kodayake gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayar da kwangilar gyara hanyoyin biyu a shekarar 2017 kan kudi sama da naira biliyan 27, aikin na tafiyar hawainiya.
A watan Mayun da ya gabata ne Gwamna Ahamdu Fintiri na Adamawa ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin karɓar bashin naira biliyan100 don aiwatar da wasu daga cikin ayyukan titunan jihar.
Gwamnati na cewa wata sabuwar hanya ce ta samun kudin shiga ta gano domin rage dogaro kan gwamnatin tarayya.














