Yahoo ya dakatar da aikinsa a China

Yahoo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yahoo ya bi layin sauran manyan kmfanonin fasaha wajen rufe harkokinsa a China saboda tsauraran dokoki

Kamafanin fasaha na Yahoo ya ce zai fice daga China, yana mai cewa yanayin kasuwanci da kuma dokokin kasar kullum suna kara zama da kalubale ta yadda ba zai iya ci gaba da aiki ba a kasar.

Yahoo ya kasance kamfanin waje na baya-bayan nan da ya takura da dokokin kasuwanci na China masu tsanani.

Tun daga jiya Talata ne kamfanin na Yahoo ya dakatar da ayyukansa a China, inda da zarar ka nemi shiga wani shafi nasa sai ka gamu da sako cewa, an daina samun damar shiga.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ya ce harkokinsa a sauran sassan duniya suna nan suna ci gaba yadda suke ba tare da wata matsala ba.

Kamfanin zai ci gaba da kasancewa mai kiyayewa tare da martaba 'yancin masu amfani da shafi da sauran ayyukansa, cikin walwala ba tare da wata takurawa ba.

Kamfanin ya kasance daya daga cikin manyan kamfanonin fasahar zamani na waje da ya yi watsi da gudanar da harkokinsa a China, ya na mai nuni da irin yanayi da dokoki masu tsananin wuya da hukumomin China ke sanya wa.

Wata sabuwar doka da za ta fara aiki a makon nan, wadda ta danganci yadda za a rika tattara bayanai, da adana su na daga matsalolin da kamfanin na Yahooo ya ce sun tilast masa barin China.

Duk da cewa dokokin ba wai sun bambanta ba ne da dokokin kare sirri a Turai, yanayi na siyasar China ya bambanta sosai, inda hukuma ke sa dokokin takaita harkoki masu tsanani.

Ana zargin wasu kamfanonin kasashen yamma da alaka da China ko kuma adana bayanai a can.

Hatta wasu kamfanonin na China ma na shan wuya da irin dokokin sa ido da hukumomin kasar ke sanyawa, a karkashin wani shiri na shekara biyar kan kiyaye tattalin arzikinta.

Haramcin da hukumomin Chinar suka sa a kan kudin intanet na Crypto ta yi gagarumar illa ga hada-hadar kudin Bitcoin, yayin da shi kuma katafaren kamfanin sayar da kaya ta intanet na kasar, Alibaba gwamnati ta ci tararsa dala biliyan 2 da miliyan 800 a frkon shekaran nan.

A watan da ya gabata kamfnin Microsoft ya sanar da matakin rufe shafinsa na harkokin da suka shafi aiki ko ma'aikata da kasuwanci, Linkedin ya ce zai dakatar da ayyukansa a China nan gaba a cikin shekarar nan.

Daman sauran shafukan sada zumunta da muhawara kamar su Twitter da Facebook tun tsawon shekaru hukumomin na China suka toshe su.

Shi kuwa shafin matambayi-ba-ya-bata na Google sama da shekara goma ya bar aiki a kasar ta China.