Rashin Android a wayoyin Huawei zai iya shafar ku?

Android Huawei

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Huawei ne kamfani na biyu mafi girma na kamfanonin wayoyi a duniya
    • Marubuci, Daga Leo Kelion
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology desk editor

Takunkumin da aka sanya wa kamfanin Huawei na rashin samun dama na amfani da manhajar Android zai shafi sabbin wayoyin kamfanin da za a gabatar a ranar Talata.

Kamfanin ya gayyaci 'yan jarida daga fadin duniya zuwa Landan domin ganin sabuwar wayarsu ta Honor 20 Series.

An sanar da BBC cewa wayoyin za su ci gaba da amfani da Andoid da kuma manhajojin kamfanin Google.

Idan ba a sasanta rikicin da ke tsakaninsu da gwamnatin Amurka ba, wayoyin kamfanin a nan gaba za su samu tsaiko na manhajoji, idan Huawei ya yanke shawarar barin amfani da Android.

Har yanzu dai ba a san ko takunkumin da Google ya sanya wa Huawei ko zai jima ba.

Huawei

Asalin hoton, Huawei

Bayanan hoto, Huawei ta aika gagarumar gayyata ga 'yan jarida domin ganin bayyana sabbin wayoyin

To yanzu yaya abin zai kasance?

Huawei ya sanar da BBC cewa ya fi son yin amfani da Android, amma ya hada wata manhaja da wayoyinta za su iya aiki a kai a matsayin madadin Android.

"Mun jima muna wani shiri a kan ko mai ka iya faruwa, amma bai faru ba a yanzu, a cewar Jeremy Thompson mataimakin shugaban kamfanin a Birtaniya.

Richard Yu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu daga cikin sabbin wayoyin Huawei na baya bayan nan